Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-29 14:26:14    
Wasu labaru game da kabilun kasar Sin

cri

---- Cikin 'yan shekaru masu zuwa, za a kebe wuri mai ni'ima na tafkin Kanas da ke jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin da ya zama lambun shan iska mafi girma na kasar.

An ce, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, matsakaicin yawan mutanen da suka je wuri mai ni'ima na tafkin Kanas domin yawon shakatawa ya karu da kashi 25 bisa 100 a kowace shekara, amma sabo da wuraren yawon shakatawa sun kasance a yankuna kadan, shi ya sa aka gamu da matsaaloli wajen karbar masu yawon shakatawa, kuma halittu masu rai suna lalacewa a kowace shekara. Bayan da aka tsara sabon shiri an ce, za a shata wasu wuraren da ke dab da tafkin Kanas cikin lambun shan iska, wato jimlar fadin lambun za ta wuce murabba'in kilomita dubu 10.

Yanzu, ana nan ana samun ci gaba da sauri wajen sha'anin yawon shakatawa na shiyyar tafkin Kanas, a shekarar da ta wuce, jihar Xinjiang ta ware kudin Sin wato fiye da Yuan miliyan 300 domin kyautata filin jirgin sama da sauran wurare masu ni'ima da ke bakin tafkin, kuma an fara karbar masu yawon shakatawa a wasu sabbin wurare masu ni'ima.

---- Domin daidaita matsalar karancin tafinta, jihar Xinjiang ta tsai da shirin tallafawa kwararrun mutane na musamman domin tallafawa kwararrun mutane majiya harsuna 2, wato wani irin harshen karamar kabila da na kabilar Han.

Wannan shiri ya tanada cewa, daga yanayin kaka na wannan shekara a jihar Xinjiang, za a dauki dalibai 200 wandanda za su mai da muhimmanci wajen koyon harshensu na kansu da kuma harshen Han, sa'an nan kuma za su nazarci harshen kabilar Uighur da na kabilar Kazak, bayan da suka shafe shekaru 4 suna yin karatu, da akwai daliban da yawansu ya kai kashi 70 cikin 100 za su ci gaba da yin karatu domin samun digiri na 2.

Jihar Xinjiang wata jiha ce wadda take da kabilu da yaruka da harsuna da yawa. Daga cikin kabilu 13 wadanda suke zama a nan tun kaka da kakani, ban da 'yan kabilar Han, sauran 'yan kananan kabilu ciki har da kabilar Uighur da Hazak da Ke'erkezi da Hui da Mongoliya da kuma kabilar Xibo wadanda yawansu ya kai kashi 60 cikin 100 bisa na jimlar mutanen jihar Xinkiang, wadanda kuma suke yin magana da harsuna da yawa.

---- Daga watan Oktoba na wannan shekara, gidan telebijin na jihar Tibet ta kasar Sin wanda aka bude shi tun shekaru 8 da suka wuce ya fara watsa shirye-shiryensa cikin harshen kabilar Tibet ba tare da tsayawa ba cikin sa'o'i 24 na kowace rana kuma ta hanyar tauraron dan adam, wannan ya zama karo na farko ne da aka watsa shirye- shiryen telebijin a kowane lokaci kuma cikin harsunan kananan kabilun kasar Sin.(Umaru)