A ran 27 ga wata, an soma taron tattaunawa a matakin karshe kan batun shimfida zaman lafiya a Darfur ta kasar Sudan a tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyoyi masu adawa da ita a birnin Surte, birnin kasar Libya da ke bakin teku. Majalisar dinkin duniya, wato M.D.D. da kungiyar tarayyar Afirka, wato AU sun shugabanci wannan taron tattaunawa tare. Kasashen dindindin 5 na kwamitin sulhu na M.D.D. da kasashen da suke makwabtaka da kasar Sudan dukkansu sun aika da wakilansu domin halartar wannan taro. Manazarta a wurin sun bayyana cewa, wannan taron tattaunawa kan batun shimfida zaman lafiya a Darfur ya samar da damar kawo karshen wutar yaki da tabbatar da zaman lafiya a shiyyar Darfur, amma ana kuma fuskantar wasu matsaloli da kalubale.
Majalisar dinkin duniya da kungiyar tarayyar Afirka da bangarorin da abin ya shafa sun shirya ayyukan sulhuntawa da yawa ta hanyar diplomasiyya domin tabbatar da ganin kiran wannan taron tattaunawa kan batun shimfida zaman lafiya a Darfur a cikin lokacin da aka tsara. A ran 21 ga watan Satumba na shekarar da muke ciki, Mr. Ban Ki-moon, babban sakataren majalisar dinkin duniya da Mr. Konare, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka sun shugabanci taro a karo na biyu tare domin batun shimfida zaman lafiya a shiyyar Darfur, inda manyan jami'ai na kasashen dindindin na kwamitin sulhu na M.D.D. da kasashe 26 na kungiyoyin tarayyar Afirka da Turai da kasashen Larabawa sun halarci wannan taro. A cikin sanarwar da aka bayar bayan taron, an nemi bangarori daban-daban da ke da nasaba da batun Darfur da su halarci ayyukan shimfida zaman lafiya a Darfur, kuma su share fagen wannan taron tattaunawa kan batun da aka shirya a Libya.
A waje daya kuma, A ran 26 ga wata, wakilan M.D.D. da kungiyar AU da ta kasashen Larabawa da na kasashen Eritarea da Libya da Masar da Chadi da suke makwabtaka da kasar Sudan sun shirya wani taron tattaunawa, inda suka yi kira ga bangarori daban-daban, musamman kungiyoyi masu adawa da gwamnatin Sudan da suke da nasaba da batun Darfur da su halarci wannan taron tattaunawa kan batun shimfida zaman lafiya a Darfur domin tabbatar da cin nasarar taron.
Jan Eliasson, wakilin musamman na M.D.D. mai kula da batun Darfur yana fatan bangarori daban-daban za su iya halartar wannan taron tattaunawa kan batun shimfida zaman lafiya a Darfur, kuma za a iya tabbatar da wata yarjejeniyar kawo karshen wuta. Ya kuma lallashe kungyoyi masu adawa da gwamnatin Sudan da su yi amfani da wannan dama domin warware matsalolin da ke addabar juna. Malam Salim, wakilin musamman na kungiyar AU kan batun Darfur ya nuna fatan alheri ga wannan taron tattaunawa. Yana ganin cewa, wannan taron zai samar da wata dama mai ma'anar tarihi kan yadda za a kawo karshen wutar yaki da tabbatar da zaman lafiya a shiyyar Darfur.
Bugu da kari kuma, kasar Libya, uwar wannan taron ta kuma bayar da wata sanarwa, inda ta nemi bangarorin da abin ya shafa da su sa kaimi ga kokarin cin nasarar wannan taron domin kawo karshen wahalolin jin kai da jama'ar Darfur suke sha tun da wuri. A ran 25 ga wata, lokacin da yake ganawa da takwaransa na kasar Libya, shugaba Bashir na kasar Sudan ya bayyana cewa, gwamnatin Sudan za ta halarci wannan taron tattaunawa kan batun shimfida zaman lafiya a shiyyar Darfur ba tare da kowane irin sharadi ba, kuma za ta hada da sauran kasashen duniya kan yadda za a ci nasarar wannan taron tattaunawa.
Amma, jama'a masu sauraro, batun Darfur yana da sarkakiya sosai, sabani iri iri sun dade suna kasancewa a tsakanin bangarori daban-daban na Sudan. A waje daya kuma, wannan taron tattaunawa yana fuskantar wasu matsaloli da kalubale. An labarta cewa, ban da gwamnatin Sudan za ta aika da wakilanta zuwa taron, kungiyoyi masu adawa da gwamnati 7 za su kuma aika da wakilansu zuwa taron. Amma har yanzu a kalla muhimman kungiyoyi masu adawa da gwamnatin Sudan guda 2 sun ce ba za su halarci wannan taro ba. Sabo da haka, manazarta suna ganin cewa, wasu muhimman kungiyoyi ba su halarci wannan taro, wannan ya ta da wasu matsaloli, kuma zai kawo illa ga taron. Ko za a iya cin nasarar wannan taro, abin da ya fi muhimmanci shi ne ko bangarori daban-daban da suke da nasaba da batun za su iya daukar wasu hakikanan matakai domin tabbatar da zaman lafiya a shiyyar Darfur? Amma ba yanayin da ya dace kadai da sauran kasashe da kungiyoyi na duniya suka kafa ba. (Sanusi Chen)
|