A ranar 21 ga watan nan da muke ciki, wato ranar Lahadi da ta wuce, an rufe babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin na karo na 17 a nan birnin Beijing babban birnin kasar Sin, tare da samun kyawawan nasarori. A kwanan nan, masu sauraronmu sun ci gaba da aiko mana sakonninsu, inda suka bayyana ra'ayoyinsu a kan taron.
Shugaba Mohammed Idi Gargajiga da ya fito daga Gombawa CRI Listeners club, jihar Gombe tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana wata wasikar da ke cewa, a madadin dukan manbobin club da ni kaina shugaban club, muna yin fatan alheri ta samun babbar nasara mai tasiri sosai a babban taron jam'iyyar kwaminis takasar Sin a karo na 17.
Lallai wannan babban lamari ne ga kasar Sin. A bayyane kowa ya sani cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen ingiza cigaban bunkasuwar kasar Sin cikin sauri, sakamakon haka jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta gabatar da kasar Sin a idon duniya ta bangarori daban daban kuma al'umar duniya sun fahimci manyan nasarori da kasar Sin ta samu daga dukkan fannoni daban daban.
Manyan shugabannin kasar Sin sun yi muhimmin tunani da suka jaddada cewa, kamata ya yi a zurfafa aikin tabbatar da ka'idar samun cigaba ta hanyar kimiyya, da sanyawa bangarori daban daban sabon kuzari, da kara karfinsu na kirkire-kirkire cikin himma da kwazo, ta yadda za'a tattara hazikanci da karfi daga duk fadin kasar Sin wajen ingiza zamantakewar al'umma mai wadata. An kuma tabo magana ta musamman kan batun yaki da almubazzaranci, dangane da wannan matsala ya kamata a yanke hukunci da yin rigakafi tare.ko shakka babu ta hanyar yin wannan babban taro ne kasar Sin zata warware duka matsalolin da suka yiwa kasar dabaibayi da samun sabbin hanyoyi na kara bunkasa sabuwar kasar Sin.
Sai kuma malam Salisu Dawanau, mai sauraronmu a ko da yaushe wanda ya zo daga birnin Abuja, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, yanzu dai an kammala Babban Taron Wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na 17. Hakika, taron bana ya ga halartar mutane masu yawa, kamar yadda aka saba. Kuma, kamar yadda muka sani, an tattauna muhimman bayanai da yawa. Fatan kowa shi ne Allah Ya sa a zartas da kudurorin da aka amince cikin nasara da samun bunkasa. Yayin da kasashe aminan kasar Sin su ma za su yi koyi da kasar wajen tattalin arzikin kasa da kuma kara yalwata a duk kan fannoni.
To, muna godiya ga wadannan sauraronmu da suka mai da hankulansu a kan taron, mun gode, kuma muna fatan masu sauraronmu za ku ci gaba da kasancewa tare da mu don sha labarai da kuma bayanai da za mu ci gaba da kawo muku dangane da taron.(Lubabatu)
|