Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-26 16:02:10    
Ana tabbatar da hasashen ' taron wasannin Olympic cikin kyakkyawan yanayi a cibiyar wasan tseren kwale-kwale ta birnin Qingdao na kasar Sin

cri

Kazalika, Mr. Li Zhipeng ya bayyana cewa, ana matukar kokari wajen yin amfani da kimiyya da kyawawan fasahohi a fannin kiyaye muhalli domin samar da kyakkyawan yanayi a lokacin da ake gina cibiyar wasan kwale-kwale na Olympic. Wadannan fasahohi sun hada da fasahar samun makamashi daga hasken rana, da fasahar yin amfani da na'ura mai aiki da karfin ruwan teku wajen samar da makamashi da kuma fasahar samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da karfin iska da dai sauransu. Mr. Li Zhipeng ya kara da cewa: " Yin amfani da wadannan nau'rori masu kiyaye muhalli zai kara fadakar da jama'a wajen fahimtar hasashen ' Taron wasannin Olympics cikin kyakkyawan yanayi'. Mun lashi takobin yin amfani da wadannan fasahohi na zamani a cikin cibiyarmu ta wasan kwale-kwale. Hakan zai bada misalin koyo sosai a duk zamantakewar al'ummar kasar".

Jama'a masu sauraro, aikin samar da ingantaccen abinci, wani muhimmin aiki ne daban dake gaban cibiyar din. Madam Shan Liang ta bayyna wa wakilinmu cewa : "Gwamnatin birnin Qingdao ta kafa wata cibiyar musamman ta samar da ingantaccen abinci. A lokaci daya, muna bukatar 'yan kasuwa masu bada hidimomi da su tafiyar da harkokinsu daidai bisa ma'aunan da abin ya shafa da ake aiwatarwa tsakanin kasa da kasa".

Yanzu, lokaci ya yi kasa da shekara guda da ta rage a gudanar da taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008. Muka cike da imanin cewa, gasar wasan kwale-kwale da za a gudunar a Qingdao za ta kasance wata kasaitacciyar gasa mai matsayin koli wadda kuma take da sigar musamman. ( Sani Wang)


1 2