Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-25 16:59:49    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin (5)

cri

----Wani tsuntsun Mynah ya nun kishi ga maigida.Mr Wang Xiangjian yana sha'awar tsuntsaye sosai.sai ya je kasuwa ya saye wasu tsuntsaye yana kiwonsu,wani tsuntsun da ake kira shi Hei Ge daga cikin tsuntsayen da ya saye ya kan bayyana dukkan alamun da wata kishiya ko buduwa mai soyayya ta kan nuna.Idan mai gida ya yi watsi da shi,sai nan da nan ya yi fushi ya tashi sama.Mr Wang daga birnin Zhengzhou na lardin Henan na kasar Sin ya saye wani tsuntsun da kudin Sin Yuan talatin a kasuwa,ya mai da hankalinsa sosai wajen kiwon tsuntsun cikin shekara daya da watanni hudu.Tsuntsun da wannan tsoho mai gidan da ke da shekaru 67 da haihuwa sun yi zaman jituwa.Wata matsala da ta dame shi ita ce duk lokacin da Mr Wang yake son karanta jarida.sai tsuntsun Hei Ge ya yi fushi kuma ya nuna kishi.Bisa labarin da Mr Wang ya kawo,an ce tsuntsun ya kan tashi ya sauka bisa kafadansa ya kan yi koto a jaridar da ya ke son karanta.Ko wace rana Mr Wang yana tare da tsuntsunsa ba ya rabu da shi,sabo da tsuntsun yana son shi kwarai da gaske.Haka ma matarsa da 'ya'yansa suna son tsuntsun sosai.

----Wani kare ya damu saboda mutuwar danuwansa.Wani karamin kare mai gashin baki ya nuna damuwarsa ya yi yajin cin abinci sabo da mutuwar danuwansa.Wannan batu ya wakana ne a gundumar Huojia na lardin Henan na kasar Sin.A wata ranar lahadi da safe karnuka biyu suna wasa a kan babbar hanyar mota dab da kauyen Xiaoguanzhuang,amma a wannan lokaci abokinsa ya mutu ba tsammani ba dalili.Karen nan mai gashin baki ya nuna juyayi ga abokinsa ba ya so ya bar gangar jikin abokinsa ba,har ma ya kin cin abinci a duk rana.

---Samari da yawa suna so su samu abokan aure.Ma'aikata na karamar hukuma ta yankin Caidian na lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin sun nuna damuwarsu kan karuwa ma'aikata samari da ba su yi aure ba tukuna a gun liyafar da aka shirya a karshen makon da ya shige.Bisa labarin da aka samu,an ce samari ma'aikata sama da dubu da dari biyu da yawan shekarunsu na tsakanin 18 da 50 sun shiga liyafar da aka shirya a wannan rana.Wannan ne karo na farko da hukumar karamar hukuma ta shirya irin wannan liyafa.Bisa sakamakon binciken da aka yi,an ce kashi 60 bisa dari na samari ma'aikata da shekarunsu sun isa aure har yanzu dai ba su yi aure ba tukuna.Dalili kuwa shi ne aiki ya yi musu yawa shi ya sa ba su samu damar ganawa da abokansu ba.

---Mutanen da suke son a tabbatar da wassiyarsu na karuwa a kasar Sin.An ce samari da yawa suna so a tabbatar da wasiyyarsu.wani malami Wu yana daya daga cikin irin mutane a cikin birnin Chengdu na lardin Sichuan na kasar Sin.Mr Wu dan kasuwa ne mai sayar da filaye da gidajeYana son dansa ya gaji gidansa mai kyau da dakunansa da kuma motarsa idan ya mutu ba tsammani.Yanzu ya rabu da matarsa yana damuwa matarsa ta yi kalubale dansa wajen gadon dukiyarsa.Da haka ya rubuta wata wassiya,ya nemi ofishin da abin ya shafa ya tabbatar da ita kan raba dukiyarsa bayan mutuwarsa.Ofishin samar da tabbaci na jama'a na yankin Shudu na birnin Chengdu ya bayyana cewa samari kamar Mr Wu wei sun yi yawa,suna so a tabbatar da wassiyarsu domin gudun matsalar raba dukiyoyi bayan mutuwarsu.

--An yi takarar neman matsayin wakilin gari.Da akwai 'yan takara guda goma suna so su samu matsayin wakilin garinsu na Sanxing na birnin Chengdu na lardin Sichuan na kasar Sin,sun shiga takara ta hanyar yin raye raye da wake wake da karanta wakoki.An shirya wannan takara ne a ranar jumma'a da ta shige a birnin Cheng.daga baya Mr Tang Min ya ci zaben ya zama wakilin garin,shi dalibi ne a jami'ar radiyo da telebiji na birnin Chengdu.Masu shirya takarar sun ce suna su samu wani wakili ne ya iya nuna ci gaban da muka samu a cikin kauye,sai a ce muna zaman jin dadi kamar mazaunan birnin.

----Wani miji ya bayar da wani kodarsa ga matarsa.Wani miji ya bayar da kodarsa ga matarsa a ranar laraba da ta shige domin murnar ranar cikon shekaru 20 da suka yi aure.Lamarin nan ya faru ne a birnin Zunyi na lardin Guizhou na kasar Sin.Matarsa malamar koyarwa tana da shekaru 45 da haihuwa.a karshen shekarar bara an gane matarsa ta kamu da cutar koda mai tsanani,idan ba a dasa mata wata koda ba sai ta mutu.Da ganin haka,mijinta Mr Luo Yufeng mai shekaru 50 da haihuwa ya kama gaba ya ba mata wata kyauta da ba wanda ke iya baiwa mata ba,ita ce kodarsa.

----An bukaci mazaunan birnin Shengyang da su yi hawan kekuna.An samar da kekunan hawa ga mutanen dake so amfani da su ba tare da biyan kudi ba bisa wani shirin da aka tsara a birnin Sheng dake arewa maso gabashin kasar Sin inda aka nemi mazaunan birnin da su bar motocinsu a gida su yi amfani kekunan hawa domin inganta yanayi.Wata kungiyar kula da kekunan hawa ta birnin ta ce kowane mai mota na iya amfani da daya daga cikin kekunansa in ya ajiye kudi kadan,wannan yana nufin cewa kowane mutum na iya amfani da keken hawa ba tare da biyan kudi ba.kuma wannan yana daya daga cikin ayyukan da ake neman yi a ranar da aka kebe na kada a yi amfani da motoci a cikin birnin.Kungiyar ta yi fatan a yi haka.Samar da kekunan hawa ga masu motoci ta yadda za su ji dadin amfani da kekunan.