Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-24 17:21:59    
Mawaka na gida da na waje sun rera wata rubutaciyyar wakar da ke da lakabi cewar "dan adam da halittu na sarrafa duniya kafada da kafada"

cri

Kwanan baya, an gama bikin rera rubutattun wakoki na kasa da kasa na karo na farko a gabar tabkin Qinghai na kasar Sin, mawakan da suka zo daga kasashe 34 na kasa da kasa sun taru gu daya tare da mawakan kasar Sin a gabar tabkin Qinghai da ke kan tudan Qinghai da Tibet, sun yi magana da harsuna iri daban daban, amma sun rera wata rubutaciyyar waka daya tare wadda ke da lakabin cewar, "dan adam da halittu na sarrafa duniya kafada da kafada.

Wata rubutaciyyar wakar tarihin Tibet mai suna sarkin Gesar tacna yaduwa a lardin Qinghai da jihar Tibet da ke kan tuddan Qinghai-Tibet na kasar Sin cikin dogon lokaci. A cikin wakar, an bayyana wani labari dangane da wani jarumi mai ban mamaki na kabilar Tibet na zamani aru aru na kasar Sin. Kwanan baya, a wani kauyen kabilar Tibet, mawaka fiye da 300 da suka halarci bikin rera rubutattun wakoki na kasa da kasa a gabar tabkin Qinghai sun je kallon shagalin rera wakar gargajiya da ke da lakabi cewar "Sarkin Gesar".

A ranar 7 ga watan Augusta ne aka yi bikin bude shagalin rera rubutattun wakokin kasa da kasa a gabar tabkin Qinghai a karo na farko , wannan ne karo na farko da kasar Sin ta shirya babban shagalin rera rubutattun wakoki na kasa da kasa. Mawakan da suka zo daga kasashe 35 ciki har da na kasar Sin sun halarci shagalin.

A ganin mawakan, tuddan Qinghai-Tibet shi ne wani yankin da keda ta'ajibi sosai, kuma za su kara sanya idannunsu a kan abubuwa da yawa tare da fahimtarsu, kuma dukan wadannan ba za su iya mantawa da su ba har duk rayuwarsu. Babban batun shagalin shi ne "Dan adam da halittu na sarrafa duniya kafada da kafada. Wanda ke daya daga cikin masu ba da sharhi kuma shahararrun masu tsara rubutattun wakoki mai suna Shu Cai ya bayyana cewa, babban batun shagalin nan na da kyau sosai, mawakan da suka zo daga kasashe fiye da goma sun taru gu daya, a hakika dai ana bukatar wani babban batun da zai iya kawar da sabani da kuma hada da zukatan kowa da kowa, wannan shi ne huldar da ke tsakanin dan Adam da halittu. Babban batun nan zai iya bayyana sosai kan huldar da ke tsakanin dan Adam mai kirki da halittu masu kyaun gani da kagowa da za su iya kasancewa har abada.

Kasar Sin babbar kasa ce da ke fitar da rubutattun wakoki mafi yawa a duniya, daga karni na 7 zuwa na 13, kasar Sin ta taba samun mawaka da yawa, kamar su Li Bai da Du Fu da Su Shi da Li Qingzhao da sauransu, a zamanin yau, kasar Sin ta sami wasu samari mawaka, babban sakataren kungiyar mawaka ta kasar Sin Mr Zhang Tongwu ya bayyana cewa, bayan da muka shiga karni na 21, rubutattun wakokin da kasar Sin ta tsara sun sami yalwatuwa sosai, yanzu, a duk fadin kasar Sin, ana kan shirya taron rera rubutattun wakoki, kuma a kowace shekara, na kan samu rubutattun wakokin da aka rubuta da yawa, har ma yawan ire-irensu ya kai 500 ko 600, ina da imani sosai ga kara wadatar da rubutattun wakoki a kasar Sin.

A karo na farko ne aka shirya shagalin rera rubutattun wakoki na kasa da kasa a gabar tabkin Qinghai , wannan ba ma kawai kasaitaccen taro ne na mawaka ba, hatta ma abu ne mafi muhimmanci da aka kafa dandalin musanya ra'ayoyi da yin ma'amalar al'adu a tsakanin mawakan kasa da kasa masu kishin rubutattun wakoki, wani mawaki na kasar Venezuela ya bayyana cewa, a wannan gami, mun sami damar yin ma'amala da juna da mawaka na wurare daban daban na duniya kuma mun yi koyi da juna a tsakaninmu. Mun zo ne daga wurare daban daban, amma dukanmu muna kasancewa a duniya daya, kuma muna more halittu gaba daya, saboda haka wannan ne babban batu mafi kyau ga shagalin nan na rera rubutattun wakoki.

A duk tsawon lokacin shirya shagalin rera rubutattun wakoki, mawaka na gida da na waje sun tafi zuwa kauyuka da makiyayya, tare kuma zuwa gabar rawayen kogi, kuma sun bayar da wata sanarwar shagalin rera rubutattun wakoki na kasa da kasa a tabkin Qinghai.

A cikin sanarwar, an maido da rubutattun wakoki bisa matsayi mai muhimmanci, a sa'I daya kuma, an mayar da darajar da kowa ya amince da ita ta girmamawar dukan dan Adam bisa matsayin sharadin farko mafi muhimmanci.(Halima)