Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-24 15:33:04    
Jakadan Sudan a Sin ya yi hangen nesa kan makomar sabbin shawarwarin shimfida zaman lafiya a Darfur

cri

A ranar 27 ga watan nan da muke ciki a birnin Tripoli, babban birnin kasar Libya, gwamnatin Sudan da dakarun da ba sa ga maciji da ita za su fara gudanar da shawarwarin shimfida zaman lafiya na sabon zagaye. Sabo da shawarwarin na iya zama na karshe da bangarori daban daban da abin ya shafa za su yi wajen daidaita batun Darfur, gamayyar kasa da kasa ke cike da kyawawan fata a kansa. Wane irin matsayi ne gwamnatin Sudan za ta dauka a gun shawarwarin, kuma ko shawarwarin na iya cimma nasarori? Domin amsa tambayoyin, wakilinmu ya yi hira da jakadan kasar Sudan a nan kasar Sin, Mr. Mirghani Mohamed Salih.

Yanzu gwamnatin Sudan ta riga ta share fage ga sababbin shawarwarin, kuma yawancin kungiyoyin da ba sa ga maciji da gwamnati ma sun sanar da shiga shawarwarin. A game da matsayin da gwamnatin Sudan za ta dauka a gun shawarwarin, Mr.Salih ya bayyana cewa,"gwamnatin Sudan na ganin cewa, ya kamata a kayyade lokacin yin taron, wato lokacin taron ya zama takamaimai, sabo da idan ba a kayyade lokacin taron ba, shawarwarin za su iya zama masu tsawo. Sa'an nan, kamata ya yi dukan kungiyoyin dakaru, ciki har da kungiyoyin da ba su taba daddale yarjejeniyar shimfida zaman lafiya da gwamnatin Sudan ba, su shiga shawarwarin, wannan na da muhimmanci sosai."

Bayan aukuwar babban rikici da aka zubar da jini a shiyyar Darfur a shekarar 2003, bisa sulhuntawar da gamayyar kasa da kasa suka yi, bi da bi ne gwamnatin Sudan da dakarun da ba sa ga maciji da ita suka gudanar da shawarwari har sau da dama. Bayan da aka rufe babban taron shawarwari a karo na biyu kan batun Darfur da aka yi a hedkwatar MDD dake birnin New York a ranar 21 ga watan jiya, babban sakataren MDD, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, kamata ya yi taron shawarwarin siyasa kan batun Darfur da za a gudanar ba da jimawa ba ya kasance mataki na karshe wajen daidaita batun Darfur. Bayan haka, shugaban kasar Sudan, Omar Hassan Ahemd al-Bashir shi ma ya bayyana fatansa a kwanan baya cewa, taron zai kasance na karshe a wajen daidaita batun Darfur, kuma zai kawo zaman lafiya a karshe. A game da wannan, jakada Salih ya ce,"kamata ya yi shawarwarin su kasance na karshe a wajen daidaita batun Darfur daga dukan fannoni. Kafin wannan dai, an taba gudanar da shawarwari da dama a manyan biranen wasu kasashen Afirka, amma duk da haka, sakamakon da aka samu daga shawarwarin ya kasance cikin takarda ne kawai. Muna fatan bisa muhimmancin da MDD da kungiyar tarayyar Afirka suka dora kan shawarwarin, za a iya kayyade lokacin shawarwarin, sa'an nan dukan kungiyoyin dakaru za su iya halartar shawarwarin. Muna kuma fatan MDD da kungiyar tarayyar Afirka za su hukunta wadanda suka kawo cikas ga shawarwarin ko kuma ki shiga shawarwarin. Muna fatan shawarwarin na karshe za su iya tabbatar da cikakken zaman lafiya a Darfur."

A kan batun Darfur, kullum gwamnatin kasar Sin na daukar matsayin kiyaye cikakken mulkin kan Sudan da kuma yankin kasar, sa'an nan a daidaita batun ta hanyar yin shawarwari cikin lumana. Jakada Salih yana ganin cewa, Sin ta taka muhimmiyar rawa a kan batun Darfur, ya ce,"muna ganin cewa, Sin ta taka kyakkawar rawa a wajen tabbatar da zaman lafiya a Darfur, gwamnatocin kasashen biyu sun cimma daidaito ta hanyar yin shawarwari, ciki har da nada Mr.Liu Guijin a matsayin wakilin musamman a kan batun Darfur da gwamnatin Sin ta yi. Mr.Liu Guijin ya kai ziyara a shiyyar Darfur har sau biyu, kuma ya sa kaimi ga daidaita batun Darfur bisa sulhutawar da ya yi a fannin diplomasiyya. Muna godiya sabo da taimakon da Mr.Liu Guijin tare kuma da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suka bayar a wajen tabbatar da zaman lafiya a Darfur."(Lubabatu)