Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-24 14:16:33    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (17/10-23/10)

cri

Ran 15 ga wata,aka kira babban taron 17 na wakilan jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin a birnin Beijing.A ran 19 ga wata ne,aka shirya taron ganawa da manema labarai a cibiyar watsa labarai ta babban taron,inda mataimakin magajin birnin Beijing kuma mataimakin shugaba mai zartaswa na kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na birnin Beijing na shekarar 2008 Liu Jingming ya bayyana cewa,a cikin shekaru 7 da suka gabata,kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing yana gudanar da babbar manufarsa ta `sabon Beijing,sabon wasannin Olimpic` bisa shirin da aka tsara.Kawo yanzu,an riga an kammala ginawar manyan ayyuka 27 dake cikin cibiyoyi da dakunan gasa 37.Ban da wannan kuma,saboda bukatun aikin bikin budewar taron wasannin Olimpic,za a kawo karshen aikin gina cibiyar wasan motsa jiki ta kasar Sin a watan Maris na shekara mai zuwa,haka kuma za a kammala saura kafin karshen wannan shekara.Yanzu dai,ana tafiyar da harkokin da abin ya shafa yadda ya kamata.Liu Jingming ya ce,a takaice dai,ana iya cewa,cibiyoyi da dakunan wasan motsa jiki na kasar Sin za su biya bukatun shirya taron wasannin Olimpic,kuma kwamitin wasannin Olimpic na kasashen duniya da kungiyoyin wasan motsa jiki na kasashen duniya da abin ya shafa sun nuna yabo ga ayyukan da kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na kasar Sin ke yi.

Ran 21 ga wata da dare,a gun zagaye na farko na gasar share fage ta shiyyar Asiya domin zabar kungiyoyin wasan kwallon kafa wadanda za su shiga gasar cin kofin duniya ta maza ta duniya da za a yi a kasar Afirka ta kudu a shekarar 2010,kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Myama da 7:0 a birnin Fushan dake kudancin kasar Sin.A ran 28 ga wannan wata,kungiyar kasar Sin da kungiyar kasar Myama za su yi zagaye na biyu na gasar a birnin Kuala Lumpur wato babban birnin kasar Malaysia.

Ran 21 ga wata,aka shirya gasar gudun dogon zango wato Marathon ta duniya ta Beijing ta shekarar 2007 a birnin Beijing,kuma wani `dan wasa daga kasar Kenya ya samu zama na farko a cikin rukuni na maza bisa awa 2 da minti 8 da dakika 8.`Yan wasa daga kasar Sin Ren Longyun da Han Gang sun samu zama na biyu da na uku.A cikin gasa ta rukunin mata,`yar wasa daga kasar Sin Chen Rong ta samu zama ta farko,sauran `yan wasa biyu daga kasar Sin Zhang Yingying da Bai Xue sun samu zama ta biyu da ta uku. ?Jamila Zhou)