A watan satumba da ya wuce, an shirya taron tattaunawa a kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin birnin Urumqi da kasashen waje a karo na 16 a birnin Urumqi, fadar gwamnatin jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin. 'Yan kasuwa na gida da waje da yawa sun halarci irin wannan taro da a kan shirya sau daya a ko wace shekara. Sabo da haka yanzu taron ya riga ya zama daya daga cikin tarurrrukan kasa da kasa don yin tattaunawa a kan harkokin tattalin arziki da cinikayya a yankin arewa maso yammacin kasar Sin.
Jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin tana kan bakin iyakar kasa ta arewa maso yammacin kasar Sin, kuma tana tsakiyar babban yankin da ke hade da nahiyoyin Asiya da na Turai. Duk girman jihar nan ya wuce muraba'in kilomita miliyan 1 da dubu 600, tsawon iyakar kasar kuma ya kai kilomita 5,600. Jihar ta yi iyaka da kasashen Rasha da Kazakhstan da Pakistan da Indiya da kuma sauran kasashe 3. Birnin Urumqi, hedkwatar jihar Xinjiang ya riga ya zama babban wurin da aka bude wa kasashen waje kofar yamamcin kasar Sin. Malam Naiyimu Yasen, magajin garin Urumqi ya bayyana cewa, "birninmu yana kan matsayi mai muhimmanci bisa taswira, 'yan kasuwa da yawa wadanda suka fito daga kasashen tsakiyar Asiya suna ta zuwa birnin don yin harkokin cinikayya, sa'an nan masu aikin masana'antu na birane masu sukuni na kasar Sin su ma sun kafa masana'antunsu kamar masakar tufafi da masana'antun yin takalma da huluna a birninmu. Jimlar kudi da birninmu ya samu daga wajen cinikin waje ya kai dalar Amurka biliyan 4.5 a shekarar 2006, wato ke nan ya karu da kashi 15 cikin dari bisa na shekarar 2005.
Tun bayan da aka fara shirya irin wannan taron tattaunawa na birnin Urumqi a shekarar 1992, an sami ci gaba cikin sauri. Yawan masana'antu na kasashe da shiyyoyi sama da 70 wadanda suka halarci irin wannan taron da aka taba shirya har sau 15 ya wuce dubu 10. jimlar kudin da aka samu wajen yin cinikin waje ma ya kai dalar Amurka biliyan 19.6. Musamman ma akwai 'yan kasuwa sama da 1,000 wadanda suka fito daga kasashen Rasha da Kazakhstan da Singapore da Indiya da Australiya da Iran da Korea ta Kudu da sauransu sun halarci taron nan da aka shirya a watan Satumba da ya wuce.
1 2
|