Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-23 17:53:48    
Kamfanin Microsoft ya amince da hukuncin da EU ta yanke masa

cri

A ran 22 ga wata, kwamitin kungiyar Tarayyar Turai, wato EU ya sanar da cewa, kamfanin Microsoft na kasar Amurka ya riga ya amince cewa zai biya tara domin yin kane-kane a kasuwa wanda kungiyar EU ta tsaida a shekara ta 2004. Sabo da haka, yanzu an kawo karshen rikicin da ya kasance a tsakanin kamfanin Microsoft da kungiyar Tarayyar Turai har na tsawon shekaru 9 domin kamfanin Microsoft ya sha kaye.

A gun wani taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, madam Neelie Kroes-Smit, memba mai kula da harkokin yin takara a kwamitin kungiyar tarayyar Turai ta ce, tana maraba da wannan zabi da kamfanin Microsoft ya yi. Ta kuma ce, kungiyar Tarayyar Turai za ta kara mai da hankali kan yadda kamfanin Microsoft zai aiwatar da alkawarinsa a hakika.

Madam Kroes Smit ta ce, kamfanin Microsoft ya riga ya yarda da aiwatar da kudurin da kwamitin kungiyar Tarayyar Turai ya tsaida a shekarar 2004, zai samar wa kamfanonin da suke yin takara a kasuwa da kamfanin Microsoft dukkan fasahohi na daidai bisa sharadin da ake amincewa rashin nuna bambanci. Sabo da haka, kayayyakin da wadannan kamfanoni suke yi za su iya hadawa da tsarin Windows na kamfanin Microsoft gaba daya.

Bayan da ya samu karar da kamfanin Micro-electronic na solar na kasar Amurka ya yi masa a shekarar 1998, kungiyar Tarayyar Turai da kamfanin Microsoft na Amurka sun yi gwagwarmaya sosai a fannin fama da yin kane-kane a kasuwa.

Manazarta suna ganin cewa, kamfanin Microsoft ya ba da kai ga kungiyar Tarayyar Turai yana da ma'ana sosai. Da farko dai, zai kawo wa kungiyar Tarayyar Turai tasiri sosai kan irin matsayin da kungiyar za ta dauka kan fama da kane-kanen da masana'antu na zamani, kamar irin wadanda kamfanin Microsoft suke yi a kasuwa. Kuma zai yi tasiri ga makomar raya masana'antun fasahohin sadarwa. Alal misali, kamfanin Intel da kamfanin Apple da sauran manyan kamfanonin fasahohin sadarwa na kasar Amurka za su fuskanci binciken da kwamitin kungiyar Tarayyar Turai zai yi musu domin fama da yin kane-kane a kasuwa. Amma wasu masanan ilmin tattalin arziki na Turai sun bayyana cewa, babu adalci ga hukuncin da kwamitin kungiyar tarayyar Turai ya yanke wa kamfanin Microsoft. Ya kamata kungiyar Tarayyar Turai su mai da hankali kan kamfanonin Cater wadanda suke sarrafa farashin kayayyaki tare a kasuwa. Amma ba kamfanoni wadanda suke dogara da fasahohinsu, kuma suke samun cigaba a kasuwa, kamar kamfanin Microsoft ba.

A waje daya, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kungiyar Tarayyar Turai ta dauki jerin kwararan matakai kan batun yin kane-kane a kasuwa. Ba ma kawai ya yanke hukunci kan kamfanin Microsoft ba, har ma ya taba yanke hukunci kan manyan masana'antun yin maganin Vitamin da na kera lift da na yin giya wadanda suke kane-kane a kasuwa, kuma ta ci su tara. A wannan karo, kamfanin Microsoft ya ba da kansa, wannan ya sake jaddada karfin kwamitin kungiyar Tarayyar Turai wajen yaki da kane-kane. Bayan kamfanin Microsoft, tabbas ne za a ci gaba da cin tara ga wasu manyan kamfanoni domin kane-kanen da suke yi a kasuwa.

Bugu da kari kuma, an ci kamfanin Microsoft tara a kasuwar Tarai, mai yiyuwa ne zai ta da matsaloli iri iri, alal misali, mai yiyuwa ne kasashen Asiya za su yi koyi da matakan da kungiyar Tarayyar Turai ta dauka domin yaki da kane-kanen da kamfanin Microsoft ke yi a kasuwannin Asiya. A kasashen Turai ma, har yanzu kamfanin Microsoft yana cikin mawuyacin hali. A wannan karo, kamfanin Microsoft ya ba da kai domin hukuncin da kwamitin kungiyar Tarayyar Turai ya yi masa a shekarar 2004, amma a tsakanin shekarar 2004 da ta 2007, kungiyar Tarayyar Turai ta taba tsai da kudurin cin tara ga kamfanin Microsoft. Madam Neelie Kroes-Smit ta bayyana cewa, kwamitin kungiyar Tarayyar Turai zai ci gaba da cin kamfanin Microsoft tara domin kamfanin bai aiwatar da hukuncin da kwamitin ya yi masa a da ba.