
Game da yadda za a bai wa masu yawon shakatawa kyakkyawar hidima da kuma kiyaye yankin Shilin yadda ya kamata, shugaba Li Zhengping na hukumar kula da shiyyar yawon shakatawa ta Shilin ya bayyana cewa, 'Hukumarmu ta soma tsara shirin raya shiyyar yawon shakatawa ta Shilin a shekarar 1985, ba a sami irin shiri da yawa a duk kasarmu ba. Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta zartas da kuma aiwatar da wannan shiri a shekarar 1987. Gundumar Shilin da gundumar Luliang ta kabilar Yi mai cin gashin kanta na lokacin can ta tsara 'ka'idojin kiyaye wuraren yawon shakatawa na gundumar Luliang' a shekarar 1991. Shirin da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta zartas da shi da kuma ka'idojin kiyayewa da hukumar wurin ta fito da su sun aza harsashi mai inganci a gare mu wajen kiyaye shiyyar Shilin.'
A shekarun baya da suka wuce, hukumar kula da shiyyar yawon shakatawa ta Shilin ta gayyaci kawarru da yawa a matsayin masu ba da shawara don raya shiyyar Shilin ta hanyar kimiyya.
Ban da wannan kuma, hukumar kiyaye muhalli na wurin kan sa ido da bincike kan yanayin iska da ruwa a shiyyar Shilin a lokaci-lokaci don tabbatar da ingancin iska a shiyyar. Dadin dadawa kuma, a kowace shekara, an shirya gagaruman harkokin yada ilmin kiyaye muhalli a kauyukan da ke dab da shiyyar Shilin don karfafa tunanin 'yan kauye na kiyaye albarkatun halittu. 1 2
|