Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-23 16:53:07    
Labarai game da wasu malamai masu koyarwa na kasar Sin

cri

Ran 10 ga watan Satumba na ko wace shekara ranar malamai ce ta kasar Sin. To, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku wasu malaman koyarwa na kasar Sin. Ko da yake ayyukansu sun sha bamban, amma horar da kwararru buri ne irin daya gare su.

Lokacin ranar malamai ta ko wace shekara, lokaci ne da sabbin dalibai na jami'o'i daban daban na kasar Sin suke yin ragista wajen shiga makarantu. A farkon wannan sabon zangon karatu, furofesa Zhang Guangdou na kwalejin gine-gine da ban ruwa na jami'ar Tsinghua kuma dan cibiyar ilmin kimiyya ta kasar Sin kuma dan cibiyar gine-gine ta kasar ya yi wa sabbin dalibansa fatan alheri cewa, ya kamata ku yi kokarin karatu domin zaman kwararru, ta yadda za ku iya bayar da gudummowa ga sha'anin gine-gine da ban ruwa ga kasarta.

Bisa matsayinsa na wani shahararren kwararren kasar Sin a fannin gine-gine da ban ruwa, Mr. Zhang Guangdou ya bayar da muhimmiyar gudummowa ga tsari da kuma fasalin aikin ban ruwa na rawayen kogi da na kogon Yangtse. Lokacin da yake yin dimbin ayyukan nazari, har kullum Mr. Zhang yana aikin koyarwa ba tare da kasala ba. A cikin shekaru fiye da 40 da ya gudanar da aikin koyarwa, yawan daliban Mr. Zhang ya zarce dubu biyar, da yawa daga cikinsu sun riga sun zama kwararru ne a fannin ban ruwa da kuma samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa. Kuma Mr. Zhang yana ganin cewa, ya kamata ilmin da malamai ke rike da shi suna kan gaba har abada. Kuma ya kara da cewa, "idan har kullum ka koyar da ilmi daga wani littafi daya tak, to kai ba malami ba ne, sai mai karanta wa dalibai littafi ne kawai. Ya kamata malamai su kara ilminsu bisa bunkasuwar kimiyya da fasaha."

Idan ana ganin cewa, nauyin da ke bisa wuyan furofesa Zhang shi ne horar da kwararru a fannin ban ruwa, to Malam Li Yuanchang da ke yin aikin koyarwa har shekaru fiye da 40 a lardin Jilin da ke arewa maso gabashin kasar Sin shi wani malami ne da ya bayar da babbar gudummowa ga bunkasuwar aikin koyarwa na kauyuka.

A shekara ta 1985, Li Yuanchang ya fara aikinsa na koyar da harshen Sinanci a cikin wata makaranta ta birnin Yushu na lardin Jilin. Kuma tun wancan lokaci, ya fara neman yin gyare-gyare kan aikin koyar da Sinanci da ya dace da halin da kauyuka ke ciki. Ya kara kwarin gwiwar dalibansa wajen shiga harkokin aikatawa a fannin zaman al'umma bayan aji, ta yadda za su iya kallon duniya da idanun kansu, da kuma yin tunani da kansu. Irin wannan dabarar koyarwa ta samu sakamako mai kyau sosai. Yan Zhaodong, wani dabili na Malam Li ya bayyana cewa, "abin da Malam Li ya koyar mana ba ilmi kawai ba, har ma da wata dabara kan yadda za a samu ilmi. Wannan wata kwarewa ce da za a iya yin amfani da ita a duk rayuwarsa."

Ban da ba da lacca, Malam Li yana yin bincike da kuma nazari kan aikin ba da ilmi na kauyukan lardin Jilin. A cikin shekaru fiye da shida da suka gabata, ya ziyarci makarantun sakandare da yawansu ya kai kashi 80 cikin dari da ke kauyuka da gudumomi na lardin, kuma ya gabatar da wani tunaninsa wajen kafa sansanin kauyuka kan horar da malamai, ta yadda malamai na makarantu daban daban na kauyuka za su iya tattaunawa kan ayyukan koyarwa tare. Bisa kokarin da yake yi, ya zuwa yanzu an riga an kafa sananonin kauyuka guda 42 a lardin, kuma kwarewar dimbin malaman kauyuka wajen aiki ta samu kyautatuwa sosai sakamakon kwasa kwasai na horaswa da suka halarta. Kuma Malam Li ya bayyana cewa, "malaman da suke aiki a kauyuka suna da buri iri daya, wato gudanar da aikin ba da ilmi kamar yadda ya kamata domin kafa tushe ga bunkasuwar al'ummarmu."

Yanzu malamai fiye da miliyan 12 suna gudanar da ayyukan ba da ilmi iri daban daban a kasar Sin. Amma ana kasancewa da gibi sosai tsakanin Sin da kasashen da ke raya sha'anin ilmi sosai a fannonin yawan malamai da kuma kwarewarsu wajen aiki. Yanzu kasar Sin tana daukar matakai masu yawa wajen kara kwarin gwiwar raya aikin horar da malaman koyarwa. A kwanan nan, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya je jami'ar horar da malamai masu koyarwa ta birnin Beijing don yin hira tare da malamai da kuma dalibai. Kuma ya bayyana cewa, ya kamata duk al'ummar kasar Sin ta girmama malamai da kuma dora muhimmanci kan raya aikin ba da ilmi domin wannan aiki ya zama wani sha'ani ne da za a nuna masa girmamawa sosai. Haka kuma ya kamata a kara kwarin gwiwar matasa na-gari wajen zama malamai har duk rayuwarsu. Kande Gao)