Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-22 20:08:31    
An zabi sabbin shugabannin kwamitin tsakiya na JKS

cri

A ran 22 ga wata da safe a nan birnin Beijing an shirya cikakken zama na farko na kwamitin tsakiya na 17 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, inda aka zabi sabuwar hukumar ba da jagoranci ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da Jia Qinglin da Li Changchun da Xi Jinping da Li Keqiang da He Guoqiang da Zhou Yongkang sun zama membobin zaunannen kwamiti na hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Haka kuma, an zabi Hu Jintao da ya ci gaba da zama kan mukamin babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar da shugaban kwamitin soja na kwamitin tsakiya na jam'iyyar.

Bayan wannan cikakken zama na farko, babban sakatare Hu Jintao da sauran sabbin membobin zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sun gana da manema labaru, inda Mr. Hu ya bayar da jawabi, ya wakilci sabbin membobi na hukumar shugabanci ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya nuna godiya ga dukkan 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin domin suna amincewa da su. Ya kuma bayyana cewa, "Tabbas ne za mu sanya jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda ke rike da ragamar mulkin kasar Sin da ta kara mai da hankali kan bunkasuwar kasar Sin a gaban kome domin neman cigaban kasar da zuciya daya. Kuma za a sa kaimi ga kokarin raya tattalin arzikin gurguzu irin na kasuwanci da siyasar gurguzu irin ta dimokuradiyya da raya al'adun gurguzu na zamani da zaman al'ummar gurguzu mai jituwa. Haka kuma za a yi kokarin sanya dan Adam a gaban kome da neman bunkasuwa bisa kimiyya ba tare da kasala ba daga dukkan fannoni."

A cikin jawabinsa, Hu Jintao ya dauki alkawarin cewa, sabbin shugabannin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za su ci gaba da tsayawa tsayin daka kan matsayin bauta wa jama'a da zuciya daya. Ya ce, "Tabbas ne za mu tsaya tsayin daka kan makasudin kafa wannan jam'iyya domin bauta wa jama'a da aiwatar da harkokin mulki domin jama'a. Za a yi namijin kokari wajen daidaita batutuwan da jama'a suka fi kulawa da kuma da nasaba da moriyar jama'a kai tsaye. Da zuciya daya ne za a yi wasu hakikanan ayyuka masu kyau domin jama'a. A waje daya, za a yi kokarin tabbatar da adalci da daidai wa daida domin zaman al'ummarmu."

Lokacin da yake batu kan manufofin diplomasiyya da kasar Sin take aiwatarwa, Hu Jintao ya ce, "Tabbas ne kasar Sin za ta ci gaba da bin manufofin diplomasiyya na zaman lafiya mai zaman kanta kuma mai mulkin kanta. Kuma tun daga farko zuwa karshe, za mu bi hanyar neman bunkasuwa cikin lumana da aiwatar da tsare-tsaren bude kofa domin neman moriyar juna tare. Haka kuma, za mu raya hadin guiwa irin ta sada zumunta da sauran kasashen duniya bisa ka'idoji 5 na zaman tare cikin lumana. Kuma za mu yi kokarin raya wata duniya mai jituwa wadda take da zaman lafiya mai dorewa da bunkasuwa."

A wannan rana da safe, sabon kwamitin da'a na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya cikakken zamansa na farko, inda aka zabi Mr. He Guoqiang da ya zama sakataren wannan kwamitin da'a.

Idan an kwatanta membobin wannan zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da na zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta jam'iyyar, za a iya gano cewa, sabbin membobi sun fi karancin shekaru. A karo na farko ne aka sami wasu sabbin membobin zaunannen kwamitin da aka haife su bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin.

An haifi Hu Jintao wanda ya kai shekaru 64 da haihuwa a watan Disamba na shekarar 1942 a lardin Anhui. Kuma ya gama karatu daga jami'ar Tsinghua da ta shahara sosai a kasar Sin. Kuma ya taba shugabancin kungiyoyin matasa biyu na kasar Sin. Yau da shekaru 5 da suka wuce, an zabe shi da ya zama babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Sin. A idon fararen hula na kasar Sin, yana kokari sosai wajen sauke nauyin da ke bisa wuyansa bisa hakikanin halin da ake ciki. (Sanusi Chen)