Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-22 20:02:05    
Shugabannin kasashen waje da na jam'iyyu masu abokai sun taya murna ga Mr. Hu Jintao da ya zama babban sakataren kwamitin tsakiya na J.K.S.

cri

Ran 22 ga wata, wasu shugabannin kasashen waje da na jam'iyyu sun taya murna ta hanyar aikawa da wasika ko buga waya ga Mr. Hu Jintao da ya sake zama babban sakataren kwamitin tsakiya na 17 na J.K.S.

Mr. Nujoma, shugaban jam'iyyar jama'ar kudu maso yammacin kasashen Afirka ta kasar Namibiya ya aiko da wasikar taya murna, inda ya ce, sake zama babban sakataren kwamitin tsakiya na J.K.S da Mr. Hu Jintao ya yi ya nuna amincin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da duk jama'ar kasar Sin suka yi masa. Ya gaskata cewa, dole ne huldar da ke tsakanin jam'iyyun biyu da kasashen biyu za su yi ta sami cigaba.

Mr. Musharraf shugaban kasar Pakistan ya aiko da wasika, inda ya taya murna ga rufe babban taro na karo 17 na J.K.S. cikin nasara, kuma ya taya Mr. Hu Jintao murna tare da sauran sababbani na kwamitin tsakiya na 17.

Mr. Voronin shugaban jam'iyyar kwaminis ta kasar Moldovan kuma shugaban kasar ya aika da wasikar taya murna cewa, Mr. Hu Jintao ya sake zama babban sakataren kwamitin tsakiya na J.K.S, da sababbin shugabannin kwamitin tsakiya wadanda sun fi karancin shekaru, da sabuwar manufar ayyuka da babban taro na 17 ya tsara sun sake nuna hadin kai a cikin J.K.S.