Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-22 17:30:07    
Kafofin watsa labaru na Hongkong da Macao sun ce babban taro na karo na 17 na JKS zai kawo babban tasiri ga bunkasuwar makomar kasar

cri
An rufe babban taro a karo na 17 na JKS a ran 21 ga wata a birnin Beijing. Jaridu na Hongkong da Macao da yawa sun bayar da bayani bi da bi a ran 22 ga wata, inda suka nuna cewa, mihimman manufofi bisa manyan tsare-tsare da babban taro a karo na 17 na JKS ya gabatar da su sun nuna alama cewa, kasar Sin ta kai wani sabon matsayi wajen aiwatar da manufar yin kwakwarima da bude kofa ga kasashen waje, kuma manufofin za su kawo babban tasiri ga bunkasuwar makomar kasar.

Jaridar Dagong ta Hongkong ta bayar da bayanin edita cewa, an tanadi akidar samun ci gaba ta hanyar kimiyya da kafa zamantakewar al'umma cikin jituwa a cikin kundin dokokin jam'iyyar kwaminis ta Sin a babban taro na karo a 17 na JKS. Wannan ya shaida cewa, jam'iyyar kwaminis ta Sin tana yin ayyuka daidai da zamani a fannin babban tunanin jagoranci, kuma an samar da abubuwa cikin sigar musamman ta Sin da ta zamani a cikin kundin dokokin jam'iyyar kwaminis ta Sin.

Jaridar Kasuwanci ta Hongkong ta bayar da sharhi cewa, samun membobin sabon kwamitin tsakiya na jam'iyyar da membobin da ba cikakku ba ya nuna alamar sauyawar kungiyar shugabanci ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin. Membobi da kuma membobin da ba cikakku ba na sabon kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin sun fi kananan shekaru da karfi da kuzari daga bangarori dabam dabam.

Jaridar 'Yan Birni ta Macao ta bayar da bayani cewa, sabbin tunanin da babban taro na karo na 17 na JKS ya gabatar sun shaida akidar samun cigaban siyasa da tattalin arziki da al'adu da shimfidar zamantakewar al'umma a duk fannoni da jam'iyyar kwaminis ta Sin ta yi yayin da take fuskantar dama da kalubale.(Zainab)