Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-22 17:07:11    
An sami ci gaba wajen yin taron tattaunawa a kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin birnin Urumqi na kasar Sin da kasashen waje.

cri

Malam Zhang Ye, mataimakin shugaban kwamitin da ke jagorancin taron tattaunawar nan ya bayyana cewa, "a cikin shekarun nan 15 da suka wuce, taron tattaunawa na birnin Urumqi ya bunkasu har ya zama wani gagarumin taron kasa da kasa mafi girma kan tattalin arziki da cinikayya a yankin arewa maso yammacin kasar Sin har ma da a tsakiyar Asiya. Sa'an nan taron ya zama wata gadar da ake bi don yin ma'amalar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasashen duniya daban daban musamman kasashen Asiya ta tsaiya da yamma da kuma kudu."

Malam Jason Park, babban manajan wani kamfanin kasar Korea ta Kudu wanda ke fitar da kayayyakin aiki masu tsabatar ruwa yana fatan kamfaninsa zai kafa tsarin sayar da kayayyakinsa a tsakiyar Asiya ta hanyar taron tattaunawar nan na birnin Urumqi. Ya bayyana cewa, "wannan ne karo na biyu da na zo jihar Xinjiang. Jihar wani wuri ne mai muhimmanci a kasar Sin bisa matsayinsa na taswira. Sa'an nan taron tattaunawa na birnin Urumqi wani taro ne mafi muhimmaci a wannan yanki. Kamfaninsa yana daya daga cikin manyan kamfanonin da ke samar da kayayyakin aiki masu tsabtar ruwa a kasar Sin. Yanzu kamfaninmu ya samu babban ci gaba a yankin arewa maso yammacin kasar Sin, muna fatan kamfaninmu zai kara samun ci gaba ta hanyar wannan taron tattaunawa na birnin Urumqi."

Malam Hu Wei, mataimakin shugaban jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin ya bayyana cewa, nan gaba, jihar za ta kara samar da kyakkyawar hidima ga 'yan kasuwa na gida da wajen, ta yadda za a raya taron tattaunawa na birnin Urumqi don ya zama wani babban taron tattanawa kan kasuwanci da cinikayya a tsakanin kasa da kasa. (Halilu)


1 2