Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-22 16:53:26    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin.

cri

---- A ran 27 ga watan Satumba, ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin ta sanar da cewa, a shekara mai zuwa kasar Sin za ta kara tallafawa dalibai masu yin bincike da yawa domin samar da kwararrun mutane ga shiyyoyin kananan kabilu, bisa shirin da aka tsayar an ce, yawan daliban da za a dauka ya kai 4,200, wato ya karu da mutane 55 bisa na wannan shekarar da muke ciki.

An fara gudanar da wannan aikin daukar dalibai masu yin bincike na kananan kabilun kasar Sin ne daga shekarar da ta wuce, kuma yawancin daliban da aka dauka sun zo ne daga larduna da jihohi da birane 12 da ke yammacin kasar Sin, kuma an mai da muhimmanci wajen daukar dalibai daga mutane 'yan kananan kabilu masu sana'o'in ba da ilmi, da kimiyya da fasaha, da aikin likitanci da fasahar sadarwa, da masu gudanar da harkokin jama'a.

Wani jami'in da abin ya shafa na ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu ana karancin kwararrun mutane sosai a shiyyoyin da 'yan kananan kabilu ke zama na kasar, sabo da haka za a ci gaba da tsayawa ga yin wannan aikin tallafin kwararrun mutane domin shiyyoyin kananan kabilu na kasar Sin.

---- Daga ran 1 ga watan Oktoba, gidan telebijin na jihar Tibet ta kasar Sin ya fara watsa shirye-shiryensa cikin harshen kabilar Tibet ba tare da tsayawa ba cikin sa'o'i 24 na kowace rana, wannan ya zama karo na farko ne da aka watsa shirye-shiryen telebijin a kowane lokaci kuma cikin harsunan kananan kabilun kasar Sin.

An fara watsa shirye-shiryen telebijin cikin harshen kabilar Tibet daga shekarar 1999. A jihar Tibet da lardunan Qinghai da Sichuan da ke yammacin kasar Sin, 'yan kallon telebijin sun fi kallon shirye-shiryen telebijin da aka shirya cikin harshen Tibet. Sabo da an watsa shirye-shiryen telebijin cikin harshen Tibet ta hanyar tauraron dan adam ne, shi ya sa 'yan kabilar Tibet da yawa da ke zama a kasashen Indiya da Nepal su ma sukan kalli wadannan shirye-shiryen telebijin, wannan kuma ya zama wata muhimmiyar hanya ce da 'yan kabilar Tibet mazauna kasashen waje ke bi don samun labarun da suka faru a jihar Tibet.

---- Jihar Xinjiang ta kasar Sin za ta ware kudin Sin wato Yuan biliyan 10 don shimfida sabbin hanyoyin motoci wadanda tsawonsu ya kai kilomita dubu 32, ta yadda zuwa shekarar 2010 za a yi kokarin shimfida hanyoyin motoci zuwa dukkan garuruwa da kauyuka in akwai yiwuwa.

Har zuwa yanzu, jimlar tsawon hanyoyin motocin kauyukan jihar Xinjiang ta kai kusan kilomita dubu 100, wato kusan a ce tsarin hanyoyin motoci yana hade da dukkan garuruwa da makiyayai da gandunan daji da kauyuka. Bayan da aka gama wannan aikin kyautata tsarin hanyoyin, manoma da makiyaya da ke zama a bakin iyakar kasa ko wurare masu nesa za su samu moriya daga cikin aikin.

Jama'a masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirin "Kananan kabilun kasar Sin." daga nan Sashen Hausa na Rediyon kasar Sin. Umaru ne ke cewa assalamu alaikum. (Umaru)