Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-22 14:25:13    
Jama'ar wurare daban-daban na kasar Sin sun taya murnar cimma nasarar rufe babban taron wakilan JKS a karo na 17

cri

Bayan da labarin cimma nasarar rufe babban taron wakilan duk kasa na Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 ya bazu a wurare daban-daban na kasar Sin, jama'a sun ji dadin wannan labari wanda ya ba su kwarin gwiwa sosai. Suna ganin cewa, muhimmin taron da aka yi a wannan gami yayin da kasar Sin ke cikin wani muhimmin mataki na yin gyare-gyare da raya kasa, babu shakka zai jagoranci jama'ar kabilu daban-daban na kasar Sin su raya zamantakewar al'umma mai wadata daga dukkan fannoni cikin nasara, haka kuma zai zamanto wata sabuwar ishara ce ga samun jin dadin zaman rayuwar jama'a.

Daraktan ofishin ayyuka na unguwar Guangzhong dake gundumar Hongkou ta birnin Shanghai Wang Liping yana mai cewa, babban taron wakilan duk kasa na Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 ya tabbatar da hanyar da za a bi wajen raya zamantakewar al'ummar kasar Sin da tattalin arzikinta, a sa'i daya kuma, ya fitar da ka'idoji daban-daban na aikatarwa, sabili da haka ne, dukkan jama'a suna jinjinawa nasarar wannan babban taro.

Wani mahukunci mai suna Qiu Shaohua na babban masana'antu na biyu na saka da rini na birnin Changsha na kasar Sin ya furta cewa, "bayanai dake shafar zamantakewar al'umma mai jituwa da babban taron wakilan duk kasa na Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 ya bayar, ya yi nuni da cewa, Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta dade tana kulawa da zaman rayuwarmu, wato mu ma'aikata ne na masana'antu masu fama da talauci, lalle wannan ya burge mu sosai kuma muna jin dadin zuciya da annashuwa sosai."

Bugu da kari, wani makiyayi wai shi Zhang Xuezhi na gundumar A Lashan ta jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta, ya fadi cewa, "babban taron wakilan duk kasa na Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 ya nemi da a raya wata kyakkyawar al'ada ta kiyaye muhallin halittu, wannan albishiri ne mai dadadawa makiyaya wadanda ke zama a wurin dausayi. Za mu rubanya kokarinmu wajen kare gidajenmu da gina su, domin bude wani sabon shafi na jin dadin zaman rayuwarmu."(Murtala)