Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-21 21:31:52    
An rufe babban taron wakilan JKS a karo na 17 cikin nasara

cri

A ran 21 ga wata, an rufe babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 a nan birnin Beijing bayan da aka kammala ajandarsa. A gun bikin rufe wannan taro, an zabi sabon kwamitin tsakiya na jam'iyyar da sabon kwamitin da'a na tsakiya na jam'iyyar. A waje daya, an zartas da rahotonnin da kwamitin tsakiya na 16 na jam'iyyar da kwamitin da'a na tsakiya na 16 na jam'iyyar suka gabatar wa babban taron da kudurin yin gyare-gyare kan Daftarin Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. A gun taron, dukkan wakilan sun yarda da a rubuta tunanin neman cigaba bisa ilmin kimiyya a cikin wannan sabon Daftarin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin.

Da karfe 9 na wannan rana da safe ne aka soma bikin rufe babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17. Mr. Hu Jintao ya shugabanci wannan babban taro.

Da farko dai, wakilai fiye da 2200 da aka zabe su ta hanyar dimokuradiyya sun jefa kuri'a a zaben sabon kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ke kunshe da membobi 204 da sauran membobi 167 wadanda ba su da cikakken iko. An kuma zabi kwamitin da'a na tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ke kunshe da membobi 127.

Sannan a gun taron, an amince da rahoton da Hu Jintao ya gabatar a madadin kwamitin tsakiya na 16 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.

"Wannan rahoto ya ba da amsa ga tambayoyin da ke jibintar wace irin tuta ce jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ta daga da kuma wace irin hanya ce jam'iyyar za ta bi da wane irin buri jam'iyyar za ta nemi cimmawa yayin da kasar Sin ta shiga cikin muhimmin lokaci wajen kara neman cigaba. A cikin wannan rahoto, an kuma tsara shirye-shirye daga dukkan fannoni kan yadda za a ci gaba da sa kaimi ga aikin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da raya zaman al'ummar gurguzu ta zamani wadda za ta kai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni. Bugu da kari kuma, a bayyane ne aka tsai da kudurin raya jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin bisa tunanin yin gyare-gyare da kirkire-kirkire."

A cikin kudurin da aka zartas a gun bikin, an ce, wannan rahoton da Hu Jintao ya bayar, sanarwar siyasa da takardar ba da jagoranci ga aiki ne da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta bayar lokacin da take hada kan al'ummomin duk kasar Sin da shugabancinsu domin tsayawa tsayin daka kan hanyar gurguzu da ke dacewa da halin musamman na kasar Sin lokacin da kasar Sin ta kai wani sabon mataki mai ma'anar tarihi. An kuma yaba wa ayyukan da kwamitin tsakiya na 16 na jam'iyyar ya yi cikin shekaru 5 da suka wuce. An bayyana cewa, bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na karo na 16, kudurai iri iri da kwamitin tsakiya na jam'iyyar ya tsaida suna kan turba.

An kuma zartas da kudurin yin gyare-gyare kan Daftarin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin. A cikin kudurin, an tabbatar da ganin "tunanin sanyan dan Adam a gaban kome da neman cigaba daga dukkan fannoni bisa ilmin kimiyya" a cikin wannan sabon Daftarin Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.

"Tunanin neman cigaba bisa ilmin kimiyya muhimmin tunani ne da aka samu bayan da aka raya ra'ayoyin neman cigaba da shugabanni zuriyoyi 3 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suka bayar. Wannan tunani yana bayyana tunanin Maxism sosai. Kuma muhimmiyyar ka'ida ce da ke ba da jagoranci ga aikin raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin."

Bayan da aka kammala dukkan ajandar babban taro, Hu Jintao ya bayar da wani muhimmin jawabi, inda ya ce, "Tarihi zai tabbatar da cewa, muhimman kududrai da shirye-shiryen da aka tsaida a gun wannan babban taro, tabbas ne za su taka rawar ba da jagoranci ga kokarin raya zaman al'ummar gurguzu ta zamani a kasar Sin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Suna da muhimmanci kwarai da gaske."

Sannan, Hu Jintao ya nuna godiya sosai ga jam'iyyun siyasa da hukumomi na kasashen waje sabo da sun aiko da sakonnin taya murnar babban taron.

An rufe babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 cikin nasara a karkashin sautin "Wakar International". (Sanusi Chen)