Kungiyar shugabannin babban taron wakilan duk kasa na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 ta shirya taro a karo na uku yau 20 ga wata da safe a nan birnin Beijing, a gun taron, an zartas da daftarin jerin sunayen membobin sabon kwamitin tsakiya, da sunayen membobin da ba cikakku ba na sabon kwamitin tsakiya, da sunayen 'yan takara masu neman zama membobin sabon na kwamitin ladabtarwa na tsakiya jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, haka kuma an gabatar da daftarin jerin sunayen ga kungiyoyin wakilai daban-daban domin su tattauna a kai.
Da yammacin yau, babban taron zai shirya taron rukuni-rukuni na kungiyoyin wakilai, domin su tattauna wannan shirin sunaye. Gobe 21 ga wata da safe, za a gudanar da zabe a hukunce a gun taron.
An labarta cewa, yayin da kungiyar shugabannin babban taron wakilan duk kasa na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 ke gudanar da taronta a karo na biyu ran 17 ga wata a nan birnin Beijing, an rigaya an zartas da shirin jerin sunayen 'yan takara, wadanda aka gabatar don su zama membobin sabon kwamitin tsakiya, da membobin da ba cikakku ba na sabon kwamitin tsakiya, da sunayen mutane 'yan takara na kwamitin ladabtarwa na tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, haka kuma an gabatar da wannan shirin sunayen mutane ga kungiyoyin wakilai daban-daban domin tattaunawa a kai. Daga bisani, kungiyoyin wakilai sun tattauna kan wannan shirin sunayen mutane a tsanake. Jiya 19 ga wata da yamma da yau 20 da safe, an shirya taron gama-gari na kungiyoyin wakilai, bisa tsarin 'yan takara sun fi guraben takara yawa, an gudanar da kwarya-kwaryar zaben membobin kwamitin tsakiya, da membobin kwamitin ladabtarwa na tsakiya, da membobin da ba cikakku ba na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Bisa ka'idar zabe ta babban taro, masu kula da aikin jefa kuri'a sun sa ido sosai kan wannan zabe, saboda haka, an samu halaltaccen sakamakon zabe a wannan zagaye.(Murtala)
|