Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-20 19:45:16    
Tabbatar da lafiyar yanayin kasa nauyi ne da ke bisa wuyan masana'antun samar da makamashi, in ji wakilin babban taron JKS

cri
Ran 19 ga wata, Malam Li Ruoping, wakilan babban taron wakilan kasa na 17 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin wanda ya fito daga masana'antun man fetur na kasar ya bayyana a Beijing, babban birnin kasar Sin cewa, bayanin da rahoton babban taron ya gabatar dangane da lafiyar yanayin kasa yana da muhimmanci ga jagorancin raya sabbin masana'antu na zamani, kamata ya yi, masana'antun samar da makamashi su kara mai da hankali ga samun bunkasuwa cikin daidaito a tsakanin dan adam da halitta da masana'antu da zaman jama'a da kuma makamashi da muhalli.

Yayin da Malam Li Ruoping ke amsa tambayar da wakilin gidan rediyo kasar Sin ya yi masa a gun taron manema labarun da cibiyar yada labaru na babban taron ta shirya, ya bayyana cewa, don tabbatar da lafiyar yanayin kasa, ya kamata, masana'antun samar da makamashi su kara kwarewarsu wajen yin kirkire-kirkire cikin cin gashin kai, kuma su kara bin darikar samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba. Kuma yana ganin cewa, kamata ya yi, masana'antun gwamnatin kasar su kara kokari wajen sauke nauyin da ke bisa wuyansu a manyan fannoni uku na siyasa da tattalin arziki da kuma zaman jama'a, yayin da suke aiwatar da harkokinsu da kyau, ya kamata su kara nuna muhimmancinsu ga zaman jama'a. (Halilu)