Babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin da ake yi a halin yanzu a nan birnin Beijing yana jawo hankulan bangarori daban daban na kasashen ketare. A kwanan baya, wakilanmu da ke kasashen Koriya ta kudu da Indiya da Faransa da kuma Amurka sun yi hira da masanan kasashen, wadanda suke ganin cewa, taron ba ma kawai yana shafar halin da Sin ke ciki yanzu da kuma bunkasuwarta a nan gaba, haka kuma zai kawo babban tasiri a kan duniya.
Kasancewarta kasar da ke makwabtaka da Sin kuma babbar abokiyar cinikinta, Koriya ta kudu ta mai da hankali na musamman a kan taron. Mr. Heungkyu Kim, wani masanin ilmin siyasa da ke kwalejin nazarin harkokin diplomasiyya da tsaro na ma'aikatar harkokin waje da ciniki ta Koriya ta kudu, ya bayyana cewa,"Tun daga shekarar 2004, kullum Sin ta zo na farko a wajen yin ciniki da Koriya ta kudu, kuma ina ganin cewa, za a ci gaba da kasancewa cikin irin wannan hali. Sabo da haka, jama'ar Koriya ta kudu da gwamnati da kuma masana na kasar suna mai da hankulansu a kan harkokin siyasa na kasar Sin."
Dokta Srikanth Kondapalli, wani shehun malami ne a cibiyar nazarin harkokin gabashin Asiya da ke jami'ar Jawaharlal Nehru da ke birnin New Delhi na kasar Indiya. Ya yi nuni da cewa, babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin na karo na 17 ya jawo hankulan bangarori daban daban na kasar Indiya, musamman ma bangaren kwararru, kuma galibinsu suna karanta Rahoton taron. Dokta Kondapalli yana ganin cewa, rahoton shugaba Hu Jintao ya dora muhimmanci a kan wadannan fannoni,"na farko shi ne samun cigaba ta hanyar kimiyya, na biyu shi ne zaman al'umma mai jituwa da kuma duniya mai jituwa, na uku kuwa shi ne dimokuradiyya da ke cikin jam'iyyar kwaminis ta Sin. A cikin jawabin shugaba Hu Jintao, na lura da cewa, ya ambaci dimokuradiyya a kalla sau 60, ciki har da dimokuradiyya da ke cikin jam'iyyar kwaminis ta Sin, dukan wadannan sun bayyana aikin da jam'iyyar kwaminis ta Sin za ta ci gaba da kammala nan da shekaru biyar masu zuwa. Bayan haka, ya kuma ambaci batun yaki da cin hanci da rashawa da batun raya gurguzu irin na kasar Sin da dai sauransu."
Mr.Gregg A. Brazinsky, wani malamin da ke kwalejin nazarin huldar da ke tsakanin kasa da kasa a jami'ar George Washington, ya ce, a cikin shekaru da dama da suka wuce, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa cikin sauri, kuma kasar ta kara ba da tasirinta sosai. Sabo da haka, al'ummar Amurka sun mai da hankulansu sosai a kan taron."Akasarin masu zuba jari na Amurka suna mai da hankali sosai a kan kasar Sin, suna nuna kulawa kan ko Sin za ta aiwatar da sabbin manufofi don sa kaimi ga bunkasuwar kasuwannin hada-hadar kudi ko kuma sanyaya shi. Wadanda ke mai da hankulansu a kan shiyyoyin siyasa kuma, suna mai da hankulansu a kan ko za a sami sauye-sauye a kan manufofin diplomasiyya na kasar Sin."
Bayan haka, babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin ya kuma zama labarin da kafofin yada labarai na kasashe daban daban ke kokarin watsawa. Jaridar NOUVELLES D'EUROPE ta Faransa wata kafar yada labarai cikin Sinanci ce mafi girma a Turai, shugaban zartaswa na jaridar, Zhang Xiaobei ya ce,"Ina ganin cewa, babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin wani babban al'amari ne a cikin harkokin siyasa na kasar Sin, wanda kuma ke shafar bunkasuwar kasar Sin a nan gaba. Sabo da haka, Sinawa mazauna kasashen waje da kafofin yada labarai na Sinawa suna mai da hankulansu sosai kan batun, har ma manyan kafofin yada labarai na kasashen ketare ma suna nuna kulawa sosai. Sabo da zaman rayuwar Sinawa mazauna kasashen waje da kuma bunkasuwar harkokinsu ba su iya rabuwa da kasar asalinsu ba.(Lubabatu)
|