Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-19 22:10:41    
Sin tana fitowa da sabon tsarin manufofi kan kauyuka

cri
Wakili a gun babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin na 17, kuma shugaban ofishin ba da jagoranci kan harkokin kauyuka na kasar Sin, Mr.Chen Xiwen ya bayyana a ranar 19 ga wata a birnin Beijing cewa, a cikin 'yan shekarun baya, sakamakon jerin manufofin baiwa manoma gantanci, yawan hatsin da ake samu a kasar Sin yana ta karuwa, haka kuma kudin shiga na manoma yana ta karuwa, abin da ya fi muhimmanci shi ne, wani sabon tsarin manufofi kan harkokin kauyuka wanda ya dace da bunkasuwar garuruwa da kauyuka yana fitowa.

Mr.Chen Xiwen ya yi wannan kalami ne a yayin da yake hira da manema labarai a cibiyar maneman labaran babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin. Ya ce, wannan sabon tsarin ya hada da janye haraji hudu da aka buga musamman kan ayyukan noma da kuma manoma, da bai wa manoma kudaden alawas kan ayyukansu na kawo albarka, da gaggauta daidaita batun ingancin ruwan sha a kauyuka, da bunkasa aikin ban ruwa a fannin aikin noma da kuma hanyoyi a kauyuka da sauransu. Sa'an nan, a yi kokarin bunkasa harkokin zamantakewar al'umma a kauyuka, ciki har da ayyukan ba da ilmi da kiwon lafiya da al'adu. (Lubabatu)