Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-19 16:43:54    
An gudanar da ayyukan kiyaye tsaron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 lami lafiya

cri
Ran 19 ga wata, mataimakin magajin birnin Beijing kuma mataimakin shugaba mai zartaswa na kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing Mr Liu Jianming ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, an gudanar da ayyukan kiyaye tsaron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 lami lafiya.

Mr Liu Jianmin ya bayyana haka a gun taron manema labaru a cibiyar yada labaru ta babban taron 17 ta jam'iyya kwamnis ta kasar Sin. Ya bayyana cewa, bisa bukatun da kwamitin shirya wasannin Olympic na kasashen duniya ya yi, kasar Sin ta tsara shirin sosai domin tsaron wasannin Olympic, kuma an riga an kafa wani tsarin ba da umurni kan kiyaye tsaron wasannin Olympic mai inganci, da zai a iya ba da jagorancin cikin sassauci, haka kuma zai iya gudanar da ayyukan cikin lokaci. A sa'i daya kuma, wasu ma'aikata da masana'antu da abin ya shafa sun yi nazari kan darussa da fasahohin ayyukan kiyaye tsaron wasannin Olympic a cikin tarihin wasannin Olympic a tsanake, kuma sun dauki jerin matakai ta fasahar zamanin a duniya.

Baicin haka, kasar Sin za ta inganta hadin gwiwa tare da gamayyar kasa da kasa wajen kiyaye tsaron wasannin Olympic, alal misali, inganta hadin gwiwa ga kungiyoyin tsaro na kasashen da suka taba shirya wasannin Olympic, da yin mu'ammala tare da kungiyoyin kiyaye tsaron wasannin Olympic na kasa da kasa da dai makamatansu, ta yadda za a iya fahimtar irin halin wajen tsaron wasannin Olympic, da ba da tabbaci ga gudanar da wasannin Olmpic lami lafiya.(Bako)