Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-19 16:35:30    
Ayyukan shirin wasannin Olympics na Beijing sun kara sa kaimi ga bunkasuwar birnin Beijing

cri
A ran 19 ga wata a birnin Beijing, Liu Jingmin, mataimakin magajin birnin Beijing kuma mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin shirya wasannin Olympics ya ce, ayyukan shirin wasannin Olympics na Beijing na shekarar 2008 sun taka mihimmiyar rawa ga bunkasuwar birnin Beijing.

Liu Jingmin ya bayar da wannan a gun taron maneman labaru da aka yi a cibiyar watsa labaru ta babban taro na karo na 17 na JKS a ran nan. Ya ce, ayyukan shirin wasannin Olympics sun kara kwarjinin Beijing a duniya, sun kuma sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki na Beijing sosai, kuma sun kara kyautata amfanin birnin Beijing, an samu cigaba mai yawa a fannin muhalli da manyan ayyukan birnin. Kazalika ayyukan shirin wasannin Olympics sun inganta ma'aunin wayewar kai na zamantakewar al'umma, sun kuma kawo wa mazauna birnin ainihin moriya.

An ce, a shekarar 2006, yawan kudadden da aka samu daga aikin samar da kayayyakin cikin gida wato GDP na birnin Beijing ya kai kudin Sin Yuan biliyan 770, wanda ya ninka na shekarar 2001 sau 2.1, kuma yawan 'yan shakatawa da suka zo Beijing daga kasashen waje ya kai fiye da miliyan 3.9, wanda ya karu da mutane miliyan daya a makamancin shekarar 2001.(Zainab)