Aminai 'yan Afrika, idan ba a manta ba, a shekarar 1932, kwamitin wasannin Olympics na duniya ya zabi birnin Berlin na kasar jamus don ya zama wurin da za a gudanar da taron waannin Olympic na 11 na shekarar 1936. A wancan lokacin, 'yan ta-kife na Nazi na kasar Jamus sun nuna fankama sosai saboda har kullum suna kyamar taron wasannin Olympis. A ganinsu, lallai za a ci mutumcin kabilar German idan 'yan wasa na Jamus sukan yi gasa tare da bakar fata a gu daya. A shekarar 1933, 'yan ta-kife na Nazi sun kwace mulkin kasar jamus. Saboda haka ne dai, yanayin siyasa na kasar Jamus ya yi matsanancin sauyi. Saboda haka, kasashe da dama suka yi ikirarin kaurace wa taron wasannin Olympic na Berlin. Sakamakon haka ne dai, kwamitin wasannin Olympic na duniya ya tura wata karamar kungiya zuwa Jamus domin yin bincike da kuma yanke shawarar cewa ko birnin Berlin ya cancanci zama wurin gudanar da taron wasannin Olympic. Abin bakin ciki shi ne, madugun 'yan Nazi Adolf Hitler ya zambaci kungiyar din da cewa wai gwamnatinsa ba za ta nuna bambanci ga Yahudawa da kuma bakar fata ba. A karshe dai, an tsaida kudurin gudanar da taron wasannin Olympic na 11 a Berlin. Amma a shekarar 1936, watanni biyu kafin a bude taron wasannin, an gudanar da wani babban taro kan kiyaye hasashen Olympic a birnin Paris na Faransa, inda kasashen Faransa, da Spain, da Amurka, da kuma Burtaniya da dai sauransu suka ki suka halarci taron wasannin yayin da aka bada shawarar gudanar da shi a Barcerona na kasar Spain. Amma ba su cimma burinsu ba saboda 'yan Fascist na Spain suka shuka barna ga taron wasannin. To, a karshe dai, an gudanar da taron wasannin Olympic na Berlin cikin lokaci wato a ran 1 ga watan Agusta na shekarar 1936.
Tun da akwai sauran lokaci kadan. Yanzu bari mu dan gutsura muku wani bayani kan ingantaccen tsarin tsaro na taron wasannin Olympic na Beijing.
Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, kwanan baya, wani babban jami'in kwamitin shirya taron wasannin Olympics na Beijing ya furta a nan Beijing, cewa yanzu ana gudanar da aikin kafa cikakken tsaron bada tsaro domin taron wasannin Olympics na Beijing lami-lafiya. Domin magance yiwuwar aukuwar matsalolin ba-zata a fannin tsaro, kwamitin shirya taron wasannin Olympics na Beijing zai dauki karin matakai a fanni kirkiro tsarin tsaro na ayyukan gina filaye da dakunan wasannin Olympics, da karfafa ayyukan yaki da ta'addanci da yunkurin tashin bama-bamai da kuma na yin musanye-musanye da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a game da ayyukan tsaro na taron wasannin Olympics na Beijng, ta yadda za a cimma makasudin " Gudanar da taron wasannin Olympics lami-lafiya".
An labarta cewa, an rigaya an samu sakamako na hakika wajen gudanar da ayyukan tsaro na taron wasannin Olympics na Beijing a shekara mai kamawa. Alala misali: an kafa hukumomin bada umurni na kungiya-kungiya da kuma tsarin gudanar da ayyuka; Ban da wannan kuma, an kaddamar da " Cikakken tsarin bada tsaro domin taron wasannin Olympics" yayin da aka bada goron gayyata ga kwararru don su gabatar da rahotannin shaidawa kan ayyukan tsaro na taron wasannin Olympic na Beijing.
Mr. Zhang Shuyuan, mataimakin babban sakataren kwamitin shirya taron wasannin Olympics na Beijing kuma mataimakin ministan tsaro na kwamitin ya fadi cewa, kirkiro wani ingantaccen tsarin bada tsaro, wani muhimmin abu ne na gudanar da taron wasannin Olympics lami-lafiya. Ya kasance da bukatu iri daban-daban na tsaro bisa bambancin halayen musamman na kowane fili da kuma kowane daki na yin gasanni. Abin farin ciki shi ne, an cimma bukatun a yunkurin gina dukkan filaye da dakunan wasanni; an kuma mayar da da matakan tsaro na dukkan filaye da dakunan wasannin a matsayin wani cikakken tsari bisa kulawar ma'aikatar tsaro ta kwamitin shirye taron wasannin Olympics na Beijing.
Mr. Zhang Shuyuan ya bayyana cewa: " Muna gudanar da aikin kirkiro tsaron tsaro ta fuskar kimiyya a fasaha tare da daukar matakan bada tabbaci ga harhada na'urorin fasaha da kuma na gina filaye da dakunana wasanni a lokaci daya. Lallai ba a taba samun irin wannan misali a sauran kasashe ba. Don haka ne dai, muka samu yabo daga kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa".
Sa'annan Mr. Zhang Shuyuan ya yi farin ciki da yin bayanin cewa, ma'anar kalmomin " taron wasannin Olympics na zaman lafiya", ita ce tabbatar da samun kwanciyar hankali lokacin da ake gudanar da taron wasannin Olympics na Beijing, da samar da kyawawan hidimomi a fannin tsaro da kuma kirkiro wani muhallin zaman jituwa mai dorewa a zamantakewar al'ummar duk kasa baki daya.
Aminai 'yan Afrika, abin da muke so mu gaya muku, shi ne yanzu ya kasance da dimbin abubuwa masu amfani a gida da waje,wadanda suke iya bada tabbaci ga gudanar da ayyukan tsaro na taron wasannin Olympics na Beijing lami-lafiya, wato ke nan yanzu ya kasance da zaman karko a kasar Sin wadda take samun bunkasuwar tattalin arziki yayin da take kyautata matsayin zaman rayuwar jama'a; Kana kuma kasashen da suka yi abokantaka da ita da kuma kwamitocin wasannin Olympics da dama dukkansu suna goyon baya a kuma taimaka wa kasar Sin wajen gudanar da ayyukan share fagen gagarumin taron wasannin Olympics na Beijing.
Amma duk da haka, wajibi ne a mai da hankali sosai kan wasu boyayyun abubuwa dake hana ruwa gudu wajen gudanar da ayyukan tsaro. Game da wannan dai, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing zai kafa wani cikakken tsarin tsaro na zamani.
A karshe dai, Mr. Zhang Shuyuan ya fadi cewa : " Kwamitin shirya taron wasannin Olympics na Beijing ya rigaya ya kafa kungiyoyi 13 masu kula da harkokin filaye da dakunan wasanni na kashi na farko, wadanda suka hada da wasu mataimakan darakan tsaro".(Sani)
|