Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-19 14:02:21    
Kasar Sin za ta dauki matakai don tabbatar da ganin kowa ya samu hidimar kiwon lafiya na yau da kullum

cri

A ran 18 ga wata a birnin Beijing, mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Sin Mr. Gao Qiang ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta tabbatar da ganin kowa ya samu hidimar kiwon kafiya na yau da kullm bi da bi ta hanyar kara kudin da aka zuba da kuma rage nauyin dake bisa wuyan mazaunan gari da sauran manufofi.

Mr. Gao ya fadi haka yayin da ya gana da maneman labaru a cibiyar watsa labaru ta babban taro na 17 na wakilan kasa na JKS. Ya furta cewa, kamata ya yi kasar ta yi kokari ta kafa babban tsarin ba da hidimar kiwon lafiya da ke shimfida birane da kauyuka, da warware batun bunkasuwar aikin kiwon lafiya a kyauyuka, da kafa tsarin ba da tabbaci ga mazaunan birane da kyauyuka da su sumu aikin kiwon lafiya da sabon tsarin hadin gwiwa kan kiwon lafiya a kyauyuka. Ya kamata ta inganta tsarin ba da hidimar kiwon lafiya da tabbatar da an ba da hidimar kiwon lafiya ba don a samu kudi ba, da kuma kafa tsarin tabbatar da ba da magunguna a birane da kyauyuka, da kafa babban tsarin tabbatar da magunguna na kasa da samar wa jama'a magunguna masu aanfani da aminci da araha don tabbatar da ingantaccen magunguna.

Mr. Hu Jintao ya fadi haka a rahotun babban taro na 17, inda ya ce, za a kafa tsarin tabbatar da kowa ya samu hidimar kiwon lafiya na yau da kullum kafin shekarar 2020. Tsarin nan ya shimfida dukan mazaunan birane da kyauyuka a kasar Sin. (Zubairu)