Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-19 12:28:14    
Sharhin masu sauraronmu a kan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin

cri

Masu karatu, kamar yadda kuka ji labarin, yanzu ana babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin a nan birnin Beijing, babban birnin kasar Sin, wanda ya kasance wani taro mai muhimmancin gaske a wajen harkokin siyasa na kasar Sin, kuma bayan da muka bayar da rahotannin taron, a kwanan nan, masu sauraronmu sun aiko mana sakonninsu, inda suka bayyana ra'ayoyinsu a kan taron.

Mamane Ada, mai sauraronmu daga birnin Yamai, jamhuriyar Nijer, ya rubuto mana cewa, kamar yadda ake zata, jawabin shugaba Hu Jintao a gaban wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a wannan taro na 17 kamar yadda jama'ar kasar Sin ta ba da hankali da mahimmanci kansa, to haka ne al'ummar sauran kasashe na duniya suka bi wannan jawabi haruffa zuwa haruffa, matani zuwa matani, domin fahimtar wannan huduba. To abubuwan da za a iyar rikewa cikin wannan jawabi su ne zan ce kan kara kyautata jin dadin al'ummar kasar Sin, da mai da hankali kan huldar Sin da sauran kasashe na duniya ta hanyar huldar kasuwanci da makamantansu. Baya da haka, shugaba Hu Jintao ya dauko zancen sauye-sauye a game da siyasar tafiyar da mulkin kasar da kuma kokowa da cin hanci da rashawa. Abun da za a ce a nan shi ne wannan taro na 17 zai yi kokarin tabbatar da wata sabuwar anniya na nema Sin wani yunkurin maida wannan kasa a doron duniya wani sha kallo watan salla da kuma zama wata magangamar cigaban kasashe a cikin wannan sabon karni na 21 da muke ciki. To, mutanen nahiyar Afrika muna fatan Allah ya tabbatar da haka domin cigaban kasar Sin shi ne cigaban namu kasashen.

Sai kuma malam Salisu Dawanau, mai sauraronmu daga birnin Abuja tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, wasu kasashen Duniya, idan aka yi taron wakilan kowace jam'iyya ce mai mulkin kasa, sau da yawa a kan tashi taron ba tare da an fahimci komai ba. Kai, tun ma daga bude taron kana iya ganin rashin tabbaci. Na lura da kyau, tun daga jiya yayin da aka bude taron Wakilan Jam'iyar Kwaminis ta kasar Sin akwai hangen-nesa da kuma sanin ya kamata a al'amarin. Batun samun nasarorin tattalin arziki mai inganci da kuma dorewa, da kuma hanyoyin ci gaban kasa da al'umarta su ne su ka mamaye abubuwan da ake tattaunawa a wannan taro na 17 na Wakilan Jam'iyar Kwaminis ta kasar Sin. Alal hakika, na san sauran masu saurarenku za su aminta da abinda zan ce game da sakamakon wannan Babban taro. Zan yi murna idan a sakamakon wannan taro aka samu sasantawa dangane da batun yankin Taiwan na kasancewarta a asalinta. A karshen wannan taro, na san kasar Sin za ta kara samun ci gaba saboda haka, fata na shi ne Allah Ya taimaki kasar Sin don ta cimma yawa-yawan bukatunta masu muhimmanci, da kuma kara kyautata zumuncinta wasu kasashen Duniya.

Akwai kuma Ibrahim Rufai Imam wanda bai bayyana mana wurin da ya fito ba, ya rubuto mana wasikar da ke cewa, babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin al'amari ne da ya shafi al'amuran jam'iyyar da kuma kasar amma. Amma za mu yi farin ciki matuka idan kun ci gaba da sanar da mu abin da ke gudana. To, Ibrahim Rufai Imam, ba shakka, muna maka alkawarin ci gaba da sanar da ku cikakkun labarai game da taron, kuma muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da mu, don shan labaran taron cikin lokaci.

Bayan haka, akwai kuma masu sauraronmu da yawa, ciki har da Ibrahim Mohammad Zaria, wadanda suka taya mu murnar taron da kuma yi wa taron fatan alheri.

To, masu sauraro, muna muku godiya da mai da hankulanku a kan taron, kuma fatan muke Allah ya sa a yi taron lafiya, kuma a gama shi lafiya tare da nasarori. Bayan haka, muna fatan masu sauraronmu za ku ci gaba da kasancewa tare da mu, don ku sha labarai da dumi-duminsu dangane da taron.(Lubabatu)