A ran 18 ga wata, Li Xueju, ministan ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ya amsa tambayoyin da 'yan jaridarmu suka bayar lokacin da ya karbi intabiyu daga dukkan 'yan jarida a cibiyar watsa labaru ta babban taro na karo na 17 na JKS, inda ya ce, a halin yanzu an karbi manoma miliyan 25 a cikin tsarin ba da tabbaci ga ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta a kasar Sin.
Li Xueju ya ce, a shekaru 10 da suka wuce, kasar Sin ta fara kafa tsarin ba da tabbaci ga ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta a birane, kuma kullum yawan mutanen birane da ke cikin tsarin ya kai fiye da miliyan 22. A shekarar bana, kasar Sin ta fara kafa tsarin ba da tabbaci ga ma'aunin zaman rayuwa a kauyuka, kuma an kiyasta cewa, a karshen shekarar, yawan manoma da ke cikin tsarin zai kai miliyan 30.
Li Xueju ya ce, ban da kafa tsarin ba da tabbaci ga ma'aunin zaman rayuwa a birane da kauyuka, kasar Sin ta kafa tsare-tsaren ba da gudummawa iri dabam dabam, a ciki har da tsare-tsaren ba da gudummawa ga mutane masu fama da bala'i da likitanci a birane da kauyuka da masu yin barace-barace da fakirai. A halin yanzu an ba da gudummawa ga mutane fiye da miliyan 150, ta yadda za a tabbatar da zaman rayuwar kungiyoyin masu fama da talauci na kasar Sin kamar yadda ya kamata.(Zainab)
|