Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-18 20:43:50    
Yanzu, kasar Sin ba ta samun bunkasuwar tattalin arziki fiye da kima

cri

Ranar 18 ga wata, Mr. Zhu Zhixin, mataimakin daraktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, yanzu kasar Sin ba ta samun bunkasuwar tattalin arziki fiye da kima a duk fannoni.

Mr. Zhu Zhixin ya yi wannan bayani ne a gun taron manema labaru da aka shirya a cibiyar watsa labaru ta babban taron wakilai na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wato J.K.S.. Ya ce, yanzu a takaice dai, an samu daidaito a tsakanin samarwa da bukatu a kasar Sin, kuma ba a jawo karuwar farashi sosai akai-akai a duk fannoni a sanadiyar haka, wato abubuwan da ake bukata sun fi yawa bisa abubuwan da ake samarwa. A waje daya kuma, sharadun da ke goyon bayan bunkasuwar tattalin arzikin kasar sun samu kyautatuwa sosai.

Bayan haka kuma, Mr. Zhu Zhixin ya bayyana a gun taron cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan kasancewar babban gibi a tsakanin mazaunan birane da na kauyuka wajen samun kudi, yanzu gwamnatin kasar na daukar matakai a jere don warware matsalar rashin daidaici a wajen samun albashi.

Gwamnatin kasar Sin ta kara nuna goyon baya ga sha'anin noma, da kauyuka, da kuma manoma, kuma ta kara zuba kudi masu yawa ga yankin da ke yammacin kasar, kazalika ta kafa tsarin tabbatar da matsayin zaman rayuwa mafi kankanta na birane da kauyuka a duk kasar. Bugu da kari kuma, ta kara karfin karbar haraji da ake bugawa a kan kudin shiga na jama'a, don daidaita yawan kudin shiga da ake samu a tsakanin jama'a.

Mr. Zhu Zhixin ya ce, yanzu gwamnatin kasar Sin na kara inganta tsari ta muhimmiyar hanyar biyan kudi bisa la'akari da gwargwardon aiki, sa'anan kuma akwai hanyoyi biyan kudi daban daban da ake aiwatarwa tare. (Bilkisu)