Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-18 15:17:44    
Masu sauraron CRI da ke ketare suna sa ido kan babban taron JKS a karo na 17

cri
Tun daga budewar babban taron JKS a karo na 17 a ran 15 ga wata a birnin Beijing, masu sauraron CRI suna karanta labaran da suka shafi wannan batu a shafin internet na CRI, kuma suna sanya idonsu sosai kan babban taro na 17 ta hanyoyin daban-daban.

Salisu Dawanau, mai sauraron sashen Hausa na CRI daga kasar Nijeriya ya aiko da sakon E-mail sau da dama don nuna fatarsa ta samun nasara a babban taron JKS a karo na 17. Ya bayyana cewa, an yi babban taro na 17 a fili kuma a bude, sabo da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana cike da imani kan makomarta, shi ya sa ya girmama jam'iyyar kwaminis ta kasa Sin mai hikima da hangen nesa da fadi gaskiya.

Musa Ozal, mai sauraron CRI daga kasar Turkey ya aika da sakon E-mail cewa, jawabin Mr. Hu Jintao ya kunshe abubuwa a dukkan fannoni, sabo da haka ya sami fahimta kan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arziki da bunkasuwar kimiyya da fasaha da kafuwar zamatakewar al'umma mai jituwa a cikin yunkurin tarihi na shekaru 30 da ke karkashin manufar bude wa kasashen waje kofa da gyare-gyare na kasar Sin.(Fatima)