Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-17 20:37:35    
Kungiyoyin wakilai na babban taro na 17 sun ci gaba da tattaunawa

cri

A ran 17 ga wata, kungiyoyin wakilai na babban taro na 17 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin sun ci gaba da tattaunawa, kungiyoyi 38 sun tattauna kan rahoton da babban sakatare Hu Jintao ya bayar a madadin kwamitin tsakiya na 16 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, da rahoto kan aiki da kwamitin tsakiya mai kula da harkokin da'a na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ya gabatar, da gyararren shirin kundin mulki na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.

Wakilai sun fadi cewa, rahoton da babban sakatare Hu Jintao ya gabatar ya bayyana a fili kan hanyar da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin take bi a yayin da take cikin muhimmin lokacin yin gyare gyare, da ra'ayin samun bunkasuwa ta kimiyya, sabo da haka ne rahoton ya zama wani abun shaida ne na Marxism, ya zama wani furuci a fannin siyasa da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta gabatar a cikin sabon zamani domin samun nasarar kafa wata zaman al'umma mai wadata a fannoni daban daban.

Game da cin hanci da rashawa, wakilan suna ganin cewa, yawancin 'yan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da jami'anta suna da kyau, kalilan ne suke cin hanci da rashawa, tabbas ne Jam'iyyar Kwaminis ta Sin za ta yi yaki da wannan matsala da kyau.(Danladi)