Yanzu a nan birnin Beijing, ana yin babban taron wakilan kasa a karo na 17 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin wadda ke kan karagar mulkin kasar. A cikin rahoton da ya gabatar a gun taron, Mr Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar ya yi bayani filla-filla a kan ra'ayin raya kasa ta hanyar kimiyya, kuma ya bayyana cewa, ya kamata, Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta kara aiwatar da ra'ayin raya kasa ta hanyar kimiyya, don tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al'umma daga dukkan fannoni, ta yadda jama'a za su ci gajiyar kyakkyawan sakamakon da aka samu wajen raya kasa tare. Wakilan babban taron sun mayar da martani sosai ga bayanin. A ganinsu, a karkashin tsarin raya kasa ta hanyar kimiyya, za a kara nuna himma ga bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar Sin da na zamantakewar al'ummarta.
Tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima da bude wa kasashen waje kofa a cikin misalin shekaru 30 da suka wuce, matsakaicin saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya wuce kashi 9 cikin dari a ko wace shekara. Babban ci gaban da kasar Sin ta samu wajen bunkasa harkokin tattalin arizki da na zamantakewar al'aumma ya jawo hankulan mutane a duniya.Amma kasar ta gamu da matsaloli wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da na zamantakewar al'umma. Malam Tan Li, wakili mahalarcin taron wanda ya fito daga birnin Mianyang na lardin Sichuan ya bayyana cewa, "yayin da ake bunkasa tattalin arziki cikin sauri, matsalolin tsimin albarkatu da na kiyaye muhalli za su tsananta sosai. Saboda haka gabatar da ra'ayin raya kasa ta hanyar kimiyya da aka yi a wannan lokaci yana da muhimmanci sosai, kuma zai ba da babban tabbaci ga samun bunkasuwa mai dorewa cikin dogon lokaci."
Ra'ayin raya kasa ta hanyar kimiyya ra'ayi ne da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta gabatar, yayin da kasar Sin ta kai wani matakin raya tattalin arziki da zamantakewar al'aummarta. Bisa bayanin da Mr Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar ya yi, ra'ayin nan wani irin ra'ayi ne don samun samun bunkasuwa mai dorewa kuma cikin daidaituwa. Babban makasudinsa shi ne don neman samun bunkasuwa, fatansa kuma shi ne mayar da moriyar jama'a a gaban kome.
Wakili mahalarcin taro Fu Chengyu, babban manaja na babban kamfanin man fetur din teku na kasar Sin yana ganin cewa, "idan kamfanoninmu na gwamnatin kasar Sin sun yi aiki da kyau wajen tsimin albarkatu da kiyaye muhalli, to za su ba da taimakon musamman wajen kara kwarewar kasar Sin don samun bunkasuwa mai dorewa. Nan da shekaru 5 masu zuwa, kamfaninmu zai kashe makudan kudade wajen yin haka."
Yanzu, kasar Sin ta riga ta tsara manufarta game da makamashi da ake amfani da shi wajen samun yawan kudi daga samar da kayayyaki wato GDP zai ragu da kashi 20 cikin dari a shekarar 2010 bisa na shekarr 2005, haka kuma yawan manyan abubuwa masu gurbata muhalli ma zai ragu da kashi 10 cikin dari a shekarar 2010 bisa na shekarar 2005. Ta haka za a canja hanyar da ake bi a wasu wurare wajen kara samun kudi daga samar da kayayyaki ba tare da kiyaye muhalli da kyau ba.
Wakilai da yawa sun bayyana cewa, yayin da ake kara aiwatar da ra'ayin raya kasa ta hanyar kimiyya, jama'a za su kara samun moriyarsu. Mr Xi Jinping, wakilan mahalarcin taron kuma sakataren kwamitin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a birnin Shanghai ya ce,"gwamnatin birnin Shanghai za ta kara samar da hidima da zuba kudade musamman domin zaman rayuwar jama'a, da mutane masu fama da wahala da kauyuka da unguwoyi masu fama da wahala, da neman daidaita matsalolin da ke jawo hankulan jama'a sosai a yanzu. Sa'an nan zai dauki wasu matakai wajen samar da magani da aikin yi da ilmi da sauransu."
Wakilai mahalartan taron suna ganin cewa, a karkashin wannan tsarin raya kasa ta hanyar kimiyya, kasar Sin za ta kara samun ci gaba mai dorewa cikin daidaituwa a tsakanin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, kana kuma da tsakanin birane da kauyuka da kuma a tsakanin shiyya-shiyya. (Halilu)
|