Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-17 14:56:47    
Wasannin fasahohi na lardin Shanxi ya jawo sha'awar mutanen Taiwan

cri

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ma'amalar al'adu da ke tsakanin lardin Shanxi na babban yankin kasar Sin da lardin Taiwan sai kara yawa take yi. Kwanan baya, an nuna nagartattun wasannin fasaha iri biyu da ke da halayen musamman na lardin Shanxi a Taiwan, wasannin sun sami matukar karbuwa daga 'yan kallo na Taiwan.

Daga karshen watan Yuni zuwa tsakiyar watan Yuli, bi da bi ne Gidan nuna wasannin fasahar raye-raye da wake-wake na lardin Shanxi da kungiyar nuna wasannin fasahar raye-raye ta lardin Shanxi suka nuna wasanninsu da ke da lakabi da cewar "Rawayen kogin da ke malala tamkar raye-rayen da aka yi" da wasan da ke da lakabi da cewar " Wasu dabinai masu tsami" a birane 5 na lardin Taiwan na kasar Sin har cikin karo 14, 'yan kallo na Taiwan da yawansu ya wuce dubu 30 sun je kallon wasannin, har ma wasu mutane sun rasa damar kallon wasannin bisa sanadiyar karancin tikitin da aka sayar. Wasu gidajen rediyo mai hoto da wasu jaridu na Taiwan da saruan kafofin watsa labaru na kasashen waje sun bayar da labarai dangane da wasannin . Wata jaridar Taiwan ta bayyana cewa, wasan da ke da lakabi da cewar "Wasu dabinai masu tsami" ya jawo sha'awar 'yan kallo na Taiwan sosai da sosai, inda suka iya more al'adar wuraren da ke bakin rawayen kogi da al'adun al'ummar kasar Sin , kuma bayan da aka kammala nuna wasannin, 'yan kallo da yawa ba su son su tashi daga inda aka nuna wasannin.

Shugabar kungiyar nuna wasannin fasahar raye-raye na irin lardin Shanxi malama Wang Xihua ta bayyana cewa, bayan wasannin da muka nuna, 'yan kallo ba su son su tashi daga inda muka nuna wasanni, abin da suka yi ya burge mu sosai da sosai, wato mun yi ban kwana da godiya har sau uku, amma ba wanda ya tashi , bayan da muka kuna dukkan fitilun da ke wurin nuna wasannin, sai 'yan kallo sun tinkari zuwa dakalin nuna wasannin don yin musafaha da 'yan wasanninmu, kuma sun neme mu da mu rattaba hannu gare su.

Mataimakiyar hukumar al'adu ta lardin Shanxi mai suna Dou Mingsheng ta bayyana cewa, wasannin da muka nuna kuma suke da halayen musamman na lardin Shanxi sun jawo sha'awar 'yana kallo na Taiwan sosai da sosai, kuma 'yan kallo nuna karbuwarsu kan wasannin da muka yi sosai, sun ce, suna jin dadi da nishadi sosai da kallon wasannin.

Lardin Shanxi yana kan rawayen tudu mai fadi sosai da ke bakin rawayen kogi na arewacin kasar Sin, yana daya daga cikin manyan wuraren da suka haifar da wayewar kai na al'ummar kasar Sin tun fil azal.

Lardin Shanxi shi ne babban lardin da ke tanade da kayayyakin tarihi da yawa, yawan gine-ginen tarihi da aka gina tun daga karni na goma zuwa yau kuma har yanzu suke kasancewa a kasar Sin ya kai kashi 70 cikin dari bisa na duk kasar , sa'anan kuma lardin yana da azurtattun fasahohin gargajiyarsa da suka hada da wasannin kwaikwayo na gargajiya da wakokin gargajiya da takardun da aka yanka ta hanyar yin amfani da almakashi da sauransu, wadanda suke samun suna sosai a duniya. A lardin Shanxi, da akwai al'adun kasuwanci wanda ke ba da zurfaffin tasiri sosai ga kasar Sin. A karni na 17 zuwa karni na 19, 'yan kasuwa na lardin Shanxi na da matsayin da ba a iya biris da shi ba wajen tattalin arzikin kasar Sin, muhimmin wurin da 'yan kasuwa na lardin Shanxi ke zama a cunkushe wato tsohon birnin Pingyao an riga an mayar da shi cikin jerin sunayen kayayyakin tarihi na al'adun duniya.

Wasan da ke da lakabin "Rawayen kogi da ke malala tamkar raye-rayen da ake yi" yake nuna halayen musamman na lardin Shanxi sosai da sosai, wasan raye-raye da ke da lakabin cewar " Wasu dabinai masu tsami" ya bayyana soyayyar 'yan kasuwa na lardin Shanxi a karshen karni na 19 zuwa farkon karni na 20, abubuwan da aka nuna a cikin wasan ya burge mutane sosai tare da tausayi sosai.

Bisa bayanin da mataimakiyar shugabar hukumarkula da al'adu ta lardin Shanxi malama Dou Mingsheng ta bayyana , an ce, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, lardin Shanxi ya yi ma'amalar al'adu sosai da Taiwan, saboda haka, mutanen Taiwan suna kara fahimci al'adun lardin Shanxi na kasar Sin, suna son kallon wasannin fasahohin lardin Shanxi , kuma lardin Shanxi shi ma yana son horar da 'yan wasannin fasahohi na Taiwan.(Halima)