Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-17 09:11:02    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(11/10-17/10)

cri
Ran 11 ga wata, a birnin Shanghai na kasar Sin, an rufe taron wasannin Olympic na musamman na lokacin zafi na kasa da kasa na shekarar 2007 mai tsawon kwanaki 10. Taron wasannin Olympic na musamman na duniya taron wasannin motsa jiki ne aka shirya wa nakasassu a kwakwalwa na duk duniya. 'Yan wasan Olympic na musamman da malaman horas da wasanni fiye da dubu 10 da suka zo daga kasashe da yankuna 160 ko fiye na duniya sun shiga wannan taron motsa jiki. Shugaba Timothy Shriver na kwamitin wasan Olympic na musamman na duniya ya nuna babban yabo kan wannan taron wasannin Olmpic na musamman mai samun cikakkiyar nasara. Ya ce, Shanghai ta samar da ingatattun na'urori da hidimomi wajen shirya taron wasannin Olympic na musamman. 'Yan wasa sun nuna gwanintarsu sosai a cikin gasanni, matsayin galibin karfin yin gasa ya fi na tarurukan wasannin Olympic na musamman da aka taba kira a da. Ra'ayin da 'yan wasa suka nuna na neman samun ci gaba ba tare da kasala ya burge mutane sosai.

Ran 11 zuwa ran 12 ga wata, a nan Beijing, an bude babban taron kafofin yada labaru na duniya a karo na 2 na taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing. Wannan ne babban taron kafofin yada labaru na karshe da aka kira kafin a bude taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai zuwa, inda wakilai 330 na manyan kamfanonin dillancin labaru na duniya da kafofin yada labaru na duniya 130 suka halarta. A lokacin taron, masu halartar taron sun saurari bayanin da aka yi game da ayyukan shirya taron wasannin Olympic na Beijing, sun kuma yi tuntuba da tattaunawa da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijng kan batun ba da hidima ga kafofin yada labaru.

A kwanan baya,wani jami'in kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya bayyana cewa, yanzu ana gina babbar cibiyar yada labaru da kauyen kafofin yada labaru da za a karbi kafofin yada labaru a lokacin taron wasannin Olympic na Beijing yadda ya kamata. An kiyasta cewa, za a fara aiki da su daya bayan daya a watan Afril zuwa watan Mayu na shekara mai zuwa.

Ran 14 ga wata, a birnin Barcelona na kasar Spain, an rufe gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon tebur ta maza ta duniya ta shekarar 2007 mai tsawon kwanaki 3. Dan wasa Wang Hao na kasar Sin ya zama zakara, wannan ne karo na farko da ya zama zakara a cikin gasar duniya.

Ran 12 ga wata, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta sami wasika daga hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Australia a hukunce. Ta tabbatar da cewa, Australia ta janye jikinta daga jerin kasashen da ke neman bakuncin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kasa ta mata ta shekarar 2011. A cikin sanarwar da ta bayar, kungiyar FIFA ta bayyana cewa, yanzu sai kasashen Canada da Jamus da kuma Peru ne kawai suke ci gaba da neman samun damar shirya irin wannan gasar wasan kwallon kafa ta mata.(Tasallah)