
Ko da yake an kashe dimbin kudi wajen sayen jar kasa, amma an yi tsimin kudi a fannoni da yawa a wannan filin wasa. Ana amfani da fitilu da kayayyakin wanka irin na tsimin makamashi a wannan filin wasa, sa'an nan kuma, ana amfani da hasken rana wajen samar da ruwa mai zafi a filin wasan, ta haka an yi tsimin dimbin makamashi.
Dadin dadawa kuma, filayen ciyayi da aka shimfida a wannan filin wasa na iya shan ruwan sama cikin sauri, ta haka, bayan awa daya da aka dauke ruwa, za a iya yin gasa. Ta hanyar bututun da ke karkashin filayen ciyayi ne aka tattara ruwan sama, an iya sake amfani da ruwa.(Tasallah) 1 2 3
|