Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-15 22:00:40    
Wasu jam'iyyun siyasa da mutanen bangaren siyasa na ketare sun taya murnar kaddamar da babban taron wakilan JKS a karo na 17

cri

Yayin da ake bude babban taron wakilan duk kasa na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17, wasu jam'iyyun siyasa da mutanen bangaren siyasa na kasashen waje bi da bi ne suka bugo waya ko aiko da sako domin taya murnar kaddamar da taron.

Daga cikin mutanen wadanda suka bugo waya ko aiko da sakon taya murna, sun hada da: shugaban kungiyar hadin kan jama'ar kasashen Asiya da Afirka Mourad Ghaleb, da babban magatakardanta Nouri Abdul Razzak Hussain, da babban sakataren jam'iyyar dimokuradiyya da gurguzu ta Afirka dake kasar Senegal Landing Savane, da shugaban jam'iyyar dimokuradiyyar zamantakewar al'umma ta kasar Japan Fukushima Mizuho, da shugaban jam'iyyar dimokuradiyya ta kasar Koriya ta Kudu Park Sang-Cheon, da babban sakataren kungiyar kawancen All India Forward ta kasar Indiya Debabrata Biswas, da shugaban jam'iyyar Awami National ta kasar Pakistan Asfandyar Wali Khan, da shugaban jam'iyyar Jatio Samajtantrik Dal ta kasar Bangladesh Hasanul Haq Inu, da shugaban jam'iyyar kwaminis ta kasar Bangladesh Manzurul Ahsan Khan, da babban sakatarenta Mujahidul Islam Selim, da ministan harkokin kasa da kasa na jam'iyyar Communist Refoundation ta kasar Italiya Fabio Amato, tare da babban sakataren jam'iyyar Democratic Action ta Bosnia da Herzegovina Amir Zukic, da dai sauransu.(Murtala)