A cikin nasa rahoto,Hu Jintao ya gabatar da sabbin manufofi na rayar kasar Sin zuwa shekara ta 2020, wato a kara kwatankwacin kudin GDP na kowane dan kasa da ninki biyu bisa na shekara ta dubu biyu,a kafa wani tsarin samar da tabbaci ga zaman mazaunan birane da na karkara gaba daya,a kawar da talauci kwata kwata, kowane dan kasa zai ci moriyar samun hidima wajen kiwon lafiya,a samar da tsare tsaren samar da kayayyaki ta hanyar tsimin makamashi da albarkatun kasa da kiyaye muhalli da hanyar karuwar arziki da hanyar yin amfani da abubuwa daban-daban yadda ya kamata., Da ya juya magana kan manufar tattalin arziki,Hu Jintao ya yi bayani kan rashin daidaicin da ake samu wajen samun hidima tsakanin mazauna birane da na karkara da na tsakanin mutanen yankuna daban daban,inda ya jaddada cewa ya kamata a mai da hankali wajen tabbatar da daidaici kan zaman jin dadi na kowa da kowa, domin cika burin nan ya kamata a kara inganta tsarin kudi na jama'a da kara zuba kudi kan fannin ba da hidima ga jama. Kan fannin raya al'adu da zamantakewa,Hu Jintao ya ce ya kamata a nace ga bin ka'idar kare hakkin jama'a a fannin al'adu ta hanyar raya harkokin al'adu na jama'a,a kara zuba kudi a fannin nan,a bunkasa harkokin al'adu a kauyuka,wurare masu nesa da birane,da manoman da suka ci rani a birane; ya kamata a bi ka'idar samar da ilimi da kiwon lafiya ga kowa da kowa, sannan gwamnati ta kara daukar nauyi na samar da tabbacin zama ga iyalai masu fama da talauci,da ba da taimako ga 'ya'yan 'yan ci rani a birane don su sami ilimi dole.
Ya kuma fada cewa ya kamata a tabbatar da tsarin samar da aikin yi bai daya ga masu aiki na birane da na karkara, da inganta tsarin samar da aikin yi da na ba da tallafi ga dukkan jama'a da ke fama da talauci. Tsarin samun kudin shiga mai daidaici,muhimmiyar shaida ce ta zaman daidaicin jama'a. Kan matsalolin da ke akwai a fannin samun kudin shiga na jama'ar kasar Sin,Hu Jintao ya ce kamata ya yi a daidaita dangantaka tsakanin samun saurin cigaba da daidaici,ya kamata a mai da hankali kan zaman daidaici.Kan shimfida tsarin demakuradiya cikin harkokin siyasa,Hu Jintao ya jaddada cewa "demakuradiyar jama'a, ita ce rayuwar tsarin zaman gurguzu. Ya kamata a bar jama'a su shiga harkokin siyasa daga dukkan sassa kuma a dukkan fannoni bisa shiri, a kara samar da ilimi wajen inganta lamirin 'yan kasa; da shimfida tsarin zaman demakuradiya da shari'a na gurguzu,da 'yanci da daidaici da na adalci; a zabi da gabatar nagartattun mutane da ba su cikin jam'iyyar kwamnis ta Sin ba a guraban shugabanci na gwamnati."
A cikin rahoton,Hu Jintao ya kuma nanata matsayin ka'ida na kullum da Jam'iyyar Kwaminis ta dauka kan batun Taiwan,a makwafin JKS,da gaske ya yi kira ga bangarori biyu dake gabar tekun Taiwan da su sa aya ga halin gaba da ke tsakaninsu da daddale yarjejeniyar zaman lafiya bisa ka'idar Sin daya a duniya. Kan huldodin Sin da kasashen waje,Hu Jintao ya bayyana cewa "kullum kasar Sin za ta bi hanyar raya kasa cikin lumana, ta kuma bi manufar bude kofa ta samu nasara tare,yayin da take raya kasarta ta kuma sa kulawa kan ci gaban sauran kasashe musamman kasashen matasa. A babi na karshe a cikin rahoton kan inganta jam'iyyar kwaminis ta Sin,Hu Jintao ya bayyana cewa kamata ya yi a sa hanzari wajen shinfida tsarin demakuradiya a cikin jam'iyya da fadada bangaren shugabannin sasssan dake kasa na jam'iyyar.
Ya kuma jaddada cewa Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta tsaya tsayin daka wajen gabatar da wadanda suka karya dokoki da tsarin da'a a gaban kotu,ta yi wa masu cin hanci hukunci mai tsananni bisa dokoki. Za a yi babban cikin kwanaki bakwai. Bisa ajandar da aka tsara,wakilan za su dudduba rahoton da Hu Jintao ya bayar da gyararren shirin tsarin dokoki na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da rahoton aikin da kwamitin da'a na tsakiya zai gabatar,da zabin sabon kwamitin tsakiya da kwamitin da'a na tsakiya Jama'a masu sauraro,kun dai saurari takaitaccen bayani kan rahoton da Hu Jintao ya bayar a babban taron wakilan kasa na kwamitin tsakiya na 17 na JKS. (Ali) 1 2
|