A gun babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin na karo na 17 da aka yi a yau 15 ga wata, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, Hu Jintao ya yi jawabi, inda ya bayyana cewa, dimokuradiyya ta jama'a rai ne na tsarin gurguzu. Dole ne a bi hanyar siyasa kamar yadda ya kamata da kuma tabbatar da ikon jama'a na kula da harkokin kasa da kuma neman cimma burin kara kuzarin jam'iyyar kwaminis ta Sin da na kasa da kuma jama'a, a yayin da ake zurfafa gyare-gyaren tsarin siyasa, sa'an nan, a inganta dimokuradiyya irin ta gurguzu, a raya kasa mai tsarin gurguzu da ke da bin kyawawan dokoki, kuma a bunkasa siyasar gurguzu.
Mr.Hu Jintao ya kara da cewa, a yayin da ake bunkasa siyasar dimokuradiyya ta gurguzu, ya kamata a inganta dimokuradiyyar jama'a, a tabbatar da ikon jama'a na kula da harkokin kasa. Bayan haka, ya kamata a kara fadakar da jama'a a kan ra'ayoyin dimokuradiyya da dokoki irin na gurguzu da 'yanci da zaman daidaici da kuma adalci, sa'an nan, a tabbatar da ikon jama'a na jin dadin dimokuradiyya, a tabbatar da manufar gudanar da harkokin kasa bisa doka daga dukan fannoni, a gaggauta raya kasa mai tsarin gurguzu da ke bin kyawawan dokoki, a kyautata tsarin sa ido, ta yadda za a iya tabbatar da yin amfani da ikon jama'a a wajen moriyar jama'a.(Lubabatu)
|