Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-15 15:35:13    
Wasu labaru game da kabilun kasar Sin

cri
---- Shekarar da muke ciki shekara ce ta cikar shekaru 20 da aka kafa makarantar middil ta Tibet da ke nan birnin Beijing, cikin wadannan shekaru 20 da suka wuce, makarantar ta yi tallafawa 'yan makarantar da yawansu ya kai fiye da 3,400 domin jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin.

Kwanan baya a nan birnin Beijing, 'yan makaranta 'yan kabilar Tibet fiye da 600 sun yi waka da rawa tare da malamansu 'yan kabilar Han domin murnar ranar cika shekaru 20 da kafa makarantar.

An ce, tun da aka kafa makarantar middil ta Tibet da ke nan birnin Beijing, da akwai 'yan makaranta 'yan kabilar Tibet wadanda yawansu ya kai fiye da 3,400 suka gama karatu daga karamar makarantar sakandare wato junior-hith school da na babbar makarantar sakandare na wannan makarantar middil, yawan 'yan karamar makarantar sakandare da suka ci gaba da yin karatu cikin babbar makarantar sekandare ya kai kashi 98 bisa 100, kuma yawan daliban da suka koma jihar Tibet don yin aiki a can bayan da suka gama karatu daga jami'ar sun kai kashi 50 bisa 100.

---- A ran 24 ga watan Satumba a birnin Berlin na kasar Jamus, an bude "bikin al'adun jihar Xinjiang" wanda gwamnatin jama'a ta jihar Xinjiang ta kabilar Uighur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin, da ofishin ba da labaru na majalisar gudanarwa ta kasar, da majalisar dokoki ta birnin Berlin ta kasar Jamus suka shirya tare.

Mr. Nuer Baikeli, mataimakin shugaban jihar Xinjiang, da Mr. Ma Canrong, jakadan kasar Sin da ke Jamus, da Mr. FreiseUlrich Freise, sakataren ma'aikatar harkokin gida na birnin Berlin da wakilai fiye da 100 da suka zo daga sassa daban-daban na kasar Sin da na Jamus sun halarci bikin bude bikin al'adun.

A gun bikin bude al'adun, Mr. Freise ya bayyana cewa, an yi wannan "bikin al'adun Xinjiang" ne a daidai lokacin cika shekaru 35 da kafa huldar diplomasiya tsakanin Jamus da kasar Si, wannan ya bayyana dangantakar aminci da hadin gwiwa wadda sai kara kyautatuwa take a kowace rana tsakanin Jamus da Sin daga fannoni daban-daban ciki har da fannin siyasa da tattalin arziki da al'adu.

---- Daga ran 1 ga watan Oktoba na wannan shekara, an fara gudanar da tsarin inshorar lafiya ga mazaunan birane da garuruwa da ke jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta daga duk fannoni, mazauna kusan dubu 200 na biranen da garuruwan jihar Tibet za su sayi tsarin inshorar lafiya.

An ce, a wannan gami an shigar da mazaunan birane da garuruwa da ba su samu aikin yi ba ciki har da 'yan makarantar sakandare da na firamare na jihar Tibet cikin tsarin inshorar lafiya ta zaman al'umma. An gudanar da wannan tsarin inshorar lafiya ga mazaunan birane da garuruwa ne bisa ka'idar radin kansu, kuma bisa hanayar hadin gwiwa ta samun kudi daga mutane masu zaman kansu da gwamnatin jihar. Bisa dokokin da aka tsayar an ce, mutane masu zaman kansu za su dauki nauyin biyan kudi na kashi 30 bisa 100, sauran kudade kuma gwamnatoti na matakai daban-daban ne za su biya.(Umaru)