Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-15 15:30:55    
Ma'aikata ta farko ta samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da tsire-tsire a kasar Sin

cri
 

Manoman gundumar sun bayyana cewa, kafin a kafa ma'aikatar samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da tsare-tsare, su kan yar da karan tsire-tsire a gonakinsu a banza. Amma yanzu ba haka ba ne, suna sayar da su ga ma'aikatar, kudin da suke samu daga karan tsire-tsiren ya yi yawa. Malam Liu Guangqiang, wani manajan ma'aikatar ya ce, "ta hanyar sayen karan tsire-tsire daga hannun manoma, ma'aikatarmu ta kan biya wa manoma kudin da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 40 zuwa 50 wato daidai da nairar Nijeriya kimanin miliyan 680 zuwa miliyan 850 a ko wace shekara. Farashin tan ya kai kudin Sin misalin Yuan 200 daidai da Naira kimanin 3,400, kuma nauyin tsire-tsiren da mu kan saye daga hannun manoma ya kai kimanin tan dubu 200 a ko wace shekara. "

Lalle, kudaden nan sun yi yawa ga wata karamar gunduma wadda aikin noma ya zama babban aikinta. Da malam Liu Chengjiang, mataimakin babban majana na ma'aikatar ya tabo magana a kan ma'aikatar, sai ya bayyana cewa, "yanzu, ma'aikatarmu tana gamsar da mu kwarai. Yawan wutar lantarki da take samar ya kan kai kilowatss dubu 720 a ko wace rana, ya zuwa ran 2 ga watan Yuni da ya wuce, jimlar wutar lantarkin da ma'aikatar ta samar ya riga ya kai kilowatss miliyan 97."

Idan an kwatanta da sakamakon da ma'aikatar ta samu a fannin tattalin arziki, abin da ya fi faranta rayukan mutane shi ne, an kyautata muhallin gundumar da wuraren da ke kewayenta. Ba ma kawai ana amfani da makamashin tsire-tsire a maimakon dimbin kwal da man fetur ba, har ma yawan hayaki mai gurbata yanayin samarin sama da ake fitarwa ya ragu sosai. Daga binciken da wani sashen hukumar makamashi ta duniya ya yi, an gano cewa, karan tsire-tsire kyakkyawan makamashi ne mai tsabta. Matsakaicin yawan sinadarin da ake kira "Sulphur" a Turance wanda ke kasancewa cikin karan tsire-tsire ya yi kasa da na kwal sosai. Idan ma'aikatar samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da tsire-tsire ta dauki matakai da dama wajen hana gurbata muhalli, to, illar da take kawo wa muhalli zai kasance kadan sosai. (Halilu)


1 2