A ran 15 ga wata, za a soma babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na karo na 17 a nan birnin Beijing. Sabo da haka, Li Dongsheng, kakakin wannan babban taro ya shirya wani taron manema labaru a ran 14 ga wata, inda ya bayyana cewa, Za a yi wannan babban taro ne tun daga ran 15 zuwa ran 21 ga watan da muke ciki. Ya zuwa yanzu an riga an gama dukkan ayyukan share fagen wannan babban taro.
Jama'a masu sauraro, babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na karo na 17 wani muhimmin taro ne da za a shirya yayin da kasar Sin ta shiga cikin muhimmin lokacin yin gyare-gyare da bude kofa. A gun wannan babban taro, za a dudduba ayyukan da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi a cikin shekaru 5 da suka wuce bayan babban taron wakilan jam'iyyar na karo na 16, kuma za a tsara sabon shiri bisa manyan tsare-tsare kan yadda za a ci gaba da yin gyare-gyare da bude kofa da raya zaman al'ummar gurguzu ta zamani a nan kasar Sin.
Mr. Li ya ce, yawan wakilan jam'iyyar wadanda ya kamata su halarci wannan babban taro, kuma suke wakiltar dukkam 'yan jam'iyyar fiye da miliyan 73 zai kai 2213. Mr. Li Dongsheng ya ce, lokacin da ake zabar wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an dauki wasu sabbin matakai domin kara shimfida dimokuradiyya a cikin jam'iyyar. Mr. Li ya ce, "Mun shimfida dimokuradiyya lokacin da ake zabar 'yan takara na kwarya-kwaryan wakilan jam'iyyar. A waje daya, bayan da aka zabi kwariya-kwariyan wakilai, an gabatar da bayanansu ga jama'a a fili ta hanyoyin da suke dacewa. 'Yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin su ne suke zabar wakilai ne ba tare da rubuta sunayensu ba."
Mr. Li ya kara da cewa, ya zuwa yanzu an riga an gama dukkan ayyukan share fagen babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na karo na 17. A ran 14 ga wata da yamma, an yi taron share fagen babban taron, inda aka tabbatar da ajandar taron, kuma aka zabi wata kungiyar shugabantar babban taron da ke kunshe da mutane 237. Za a yi babban taro ne a karkashin shugabancin kungiyar.
Mr. Li Dongsheng ya ce, a gun babban taron, za a saurari da dudduba rahoton da kwamitin tsakiya na 16 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da sauraro da dudduba rahoton da kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar za su gabatar. A waje daya, za a dudduba da zartas da shirin yin gyare-gyare kan Daftarin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da zabar kwamitin tsakiya na 17 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da zabar kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar da dai makamatansu.
Wannan babban taro ya jawo hankulan kafofin watsa labaru na gida da na sauran kasashen duniya masu dimbin yawa. Ya zuwa yanzu, manema labaru fiye da 1100 wadanda suka zo daga kasashe da yankuna fiye da 50 sun gabatar da takardun neman izinin watsa labarun wannan babban taro. A waje daya, manema labaru fiye da dari 8 na kafofin watsa labaru na kasar Sin suna kuma watsa labarun wannan babban taro. Li Dongsheng ya ce, wannan babban taro yana samar wa manema labaru hidimomi iri iri domin manema labaru za su iya watsa labaru cikin sauki.
"Za mu ci gaba da aiwatar da 'Ka'idoji kan yadda manema labaru na sauran kasashen duniya za su iya watsa labaru a kasar Sin lokacin da ake yin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics a Beijing'. Za mu ba su kyawawan hihima lokacin da suke nema da watsa labaru a kasar Sin."
Bisa shirin da ofishin shirya wannan babban taro, manema labaru za su iya halarta da sauraron bikin kaddamar da taro da na rufe taron. A waje daya, manema labaru za su iya kai ziyara ga wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin idan sun samu izini. Bugu da kari kuma, cibiyar watsa labaru ta babban taron ta kafa wani shafin internet game da wannan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin domin manema labaru. (Sanusi Chen)
|