Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-14 16:23:38    
Kungiyoyin wakilai 38 da za su halarci babban taron wakilan JKS na karo na 17 sun yi rajista

cri

Za a soma babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na karo na 17 a ran 15 ga wata a nan Beijing. Ya zuwa ran 13 ga wata da dare, dukkan kungiyoyin wakilai 38 da za su halarci wannan muhimmin taro sun yi rajista.

Wakilai sun bayyana cewa, tun bayan da aka bude babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na karo na 16 a shekarar 2002 har zuwa yanzu, kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ya mayar da Hu Jintao a matsayin babban sakatare ya jagoranci al'ummar kabilun kasar da su yi hadin gwiwa da kuma gwagwarmaya tare, su aiwatar da tunanin raya kasa ta hanyar kimiyya yadda ya kamata, su kuma mai da hankulansu sosai kan raya kasa da kuma neman samun bunkasuwa da zuciya daya. A cikin shekaru 5 da suka wuce, kasar Sin ta yi ta karfafa karfinta na tattalin arziki da sauran dukkan fannoni, ta kuma ci gaba da ba da tasiri a tsakanin kasashen duniya. Sa'an nan kuma zaman rayuwar jama'ar Sin ya yi ta samun kyautatuwa, kasar Sin ta bunkasa tattalin arziki da ayyukan siyasa da al'adu da zaman al'ummar kasa na gurguzu daga dukkan fannoni. Wakilan suna fatan babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 da za a bude ba da jimawa ba zai kara kawo wa kasar Sin jituwa da bunkasuwa, sun kuma yi imanin cewa, bayan wannan muhimman taro, kasar Sin za ta kara fuskantar kyakkyawar makoma a fannin raya kanta.(Tasallah)