Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-12 17:13:22    
Taron wasannin Olympics na musamman

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malama Zainab Abbas, mazauniyar birnin Yola da ke jihar Adamawa, tarayyar Nijeriya. Malama Zainab ta turo mana wata wasika a kwanan baya da cewa, na ji labarinku cewa, ba da jimawa ba, za a gudanar da taron wasannin Olympics na musamman a birnin Shanghai na kasar Sin, to, shin mene ne ake nufin da taron wasannin Olympics na Musamman?

Gaskiyarki, malama Zainab, kamar yadda kika ji labarin, a hakika, yanzu 'yan wasa da malaman wasa fiye da dubu 10 da suka zo daga kasashe da shiyyoyi sama da 160 suna haduwa a birnin Shanghai, wato birni mafi girma a kasar Sin, domin halartar taron wasannin Olympics na musamman da ake yi a birnin, wato tun daga ran 2 har zuwa 11 ga watan nan da muke ciki. To, domin amsa tambayar malama Zainab, a cikin shirinmu na yau, bari mu bayyana muku takaitaccen tarihin wasan nan na Olympics na muamman.

Masu sauraro, taron wasannin Olympics na musamman wasanni ne da a kan gudanar musamman domin masu nakasa a kwakwalwa, kuma madam Eunice Kennedy Shriver, 'yar kasar Amurka, kuma mataimakiyar shugabar zartaswa ta asusun Kennedy ita ce ta ba da shawarar gudanar da wasannin.

'yar uwar Eunice ita ce Rosemary Kennedy, wadda ke fama da nakasa a kwakwalwa. Domin neman warkar da ita, an taba yi mata tiyata, amma an fadi. Har ma, Rosemary ta kara nakasa a kwakwal.

A shekarar 1957, bayan da Madam Eunice Kennedy Shriver ta fara kula da asusun Kennedy, sai ta fara dukufa a kan kiyaye hakkokin masu nakasa a kwakwalwa. A shekarar 1963, a lambun gidanta ne, Madam Eunice ta gudanar da wasannin motsa jiki da ke da halartar masu nakasa a kwakwalwa su 35, a cikin makonni uku da aka yi ana gudanar da wasannin, dukan masu nakasa a kwakwalwa, ciki har da Rosemary, wato 'yar uwar Eunice, sun ji dadi sosai. Abin ya burge Madam Eunice kwarai da gaske, har ma ta ci gaba da gudanar da wasanni da kuma bunkasa su shekara da shekaru.

A watan Yuni na shekarar 1968, a karo na farko ne aka gudanar da taron wasanni na musamman na duniya a birnin Chicago na kasar Amurka. Daga baya, Madam Eunice ta ci gaba da gudanar da wasannin a shekaru biyu biyu. Bayan Madam Eunice ta yi tsawon shekaru 20 tana gudanar da wasannin ba tare da tsayawa ba, kokarinta ya sami amincewa daga bangaren wasannin motsa jiki na duniya.

A watan Faburairu na shekarar 1988, Juan Antonio Samaranch, wanda a lokacin ke kan kujerar shugaban kwamitin kula da wasannin Olympics na duniya, ya rattaba hannunsa a kan wata muhimmiyar yarjejeniya, wadda ta amince da gudanar da taron wasanni na musamman na duniya da sunan "Olympics".

A ran 24 ga watan Mayu na shekarar 2002, kwamitin kula da wasannin Olympics na musamman na duniya ya sanar da cewa, birnin Shanghai na kasar Sin ya sami damar karbar bakuncin gudanar da taron wasannin Olympics na musamman na lokacin zafi na karo na 12 a shekarar 2007. wannan kuma ya zama karo na farko da za a gudanar da wasannin a Asiya da kuma kasashe masu tasowa, kuma babban jigon wasannin na wannan karo shi ne "I Know I Can", wato "Na san zan iya".(Lubabatu)