Jama'a masu saurro,barkanku da war haka,barkammu da saduwa da ku a cikin wannan sabon shirinmu na labaru masu ban sha'awa.Wannan karo na farko ne da za mu gabatar muku da irin wadannan labarai.Bayan da kuka saurara,muna fatan za ku rubuto mana wasiku inda za ku gwada ra'ayinku game da wannan shirin.
-----direba mai hikima ya fi barayi wayo: wata mata a birnin Hefei na lardin Anhui na kasar Sin ta yi sa'a ta samu kudinta mai yawan da barayin suka sata a cikin motar bus sabo da direban ya nuna mata alama.
Direban nan sunan iyalinsa Yang ya tsayar da motar bus nan da nan da kirawo 'yan sanda su zo bayan da ya san wata mata ta rasa kudinta na kudin Sin RMB yuan dubu biyar.Direban nan ya sani shi bai tsayar da motar ba bayan motar da ta yi hassara ta shiga mota,yana tsammanin tabban ne barayi na cikin motar.Direaban ya yi wa mau hawan motar bayani kan batun nan,a sa'I daya kuma ya lalashi wadanda suka yi satar kudin da su mayar da su ga matar.bayan mintoci kadan masu hawan motar sun gano akwai kudin a dabar motar.A wannan lokaci 'yan sanda ma sun isa wurin bayan da suka yi bincike suka yi gaba da mutane biyu da aka yi tuhumarsu da satar kudin a ofishin caji.
----Direban motar taxi yana neman taimako:wata rana da gangan wani direban motar taxi ya karya dokokin da aka kafa domin zirga zirgan motoci a birnin duk domin jawo hankulan 'yan sanda da su hana wata mata da take neman kashe kanta.
A ranar talata da ta shige,bayan da wata mata ta shiga motar taxi ta fashe da kuka,kuma ta bukaci direban da ya tuka motar zuwa gadar da ke bisa kogin Yangtze wanda ya fi shahara a gida da waje.Daga nan direban yana nuna damuwa kan matar,sai ya yi ta kunna wutar motarsa da tuka mota sannu a hankali duk domin jawo hankulan 'yan sanda.Bayan da 'yan sanada suka ga alama,sai sun tsayar da motarsa da yi masa tambaya.Direban ya sanar da 'yan sanda abin da ya gani.
Daga baya matar ta amince da cewa ta yi shirin daka tsalle cikin ruwan kogin Yangtse domin kashe kanta saboda ta yi musu mai tsananni da mijinta.
----Wani manomi ya mayar da kudin taimako?Wani manomi da ake kira shi Feng Baoshan a kauyen Fenglaozhuang karkashin mallakar birnin Zhumadinan na lardin Henan ya dau mota zuwa birnin Shenzhen na lardin Guangdong domin mayar da kudin taimako ga kungiyar ba da taimako ta birnin bayan da dansa ya mutu a sanadin cutar sankarar jini.
Yayin da dansa ya yi aiki a birnin Shenzhen ya kamu da cutar sankarar jini a wannan shekara,sai manomin nan mai talauci ya samu kudin taimakon da ya kai kudin Sin RMB yuan 16,300 daga mazaunan birnin Shenzhen.
Bayan da dansa ya rasu yana raguwar kudi Yuan 4050.Manomin Feng ya ce zai mayar da kudin ga wadanda suka bayar da kuma nuna musu godiya da zuciya daya.
---Kada a karya dokokin da ake bi wajen tafiye tafiye.Bisa binciken da aka yi a birnin Zhengzhou na lardin Henan na kasar Sin,an ce kimanin kashi saba'in bisa dari na matafiya a kan titi sun ce idan suna jirar nuna alamar launin tsanwa,sa'an nan su ketare hanya,su wawaye ne.
Yawancin mutanen da aka yi musu bincike wadanda suka karya dokokin tafiye tafiye suna tsammanin 'yan sanda ba za su yi musu tara ba sai wadanda suka aikata mugunta.
Ofishin kula da harkokin zirga zirgan motoci a birnin ne ya dau nauyin bincike kan mutane dari da suka kan yi tafiya a kan hanya.
Sama da mutane dubu biyu aka yi gaba da su zuwa cajin ofishi na 'yan sanda saboda ba su bi doka ba yayin da suke ketare hanya.
----wani injiniya ya kago wani abun kama kudaje.Da akwai wani injiniya da ake kira Liu Yuxing mai yawan shekaru 68 da haihuwa a birnin Wuhan na lardin Hubei na kasar Sin.Ya ce ya kago wani abu mai amfani sosai wajen kama kudaje.Abun nan ya jawo hankalin kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing.
Bisa labarin da aka samu,an ce wanan abu kamar tarko da wannan injiniya ya kago na iya kama kudaje sama dubu a rana daya.
Kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya tura kwararru biyu zuwa birnin Wuhan inda injiniya Liu ya ke zaune.Mr Liu ya yi ritaya daga kamfanin narke karfuna na birnin Wuhan.
Kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya yi shirin amfani da abun da injiniya Liu ya kago a manyan wurare biyu na tara juju a yayin da ake yin wasannin Olympics a shekara ta 2008 a birnin Beijing.
----Ma'aikatan gidan dabobi na jiran haihuwar jaririn giwa.Gidan dabobi na birnin Haikuo na lardin Hainan ya yi cigiyar kwararru da likitocin dabobi a duk kasa baki daya da su ba da taimako wajen gano dalilin da ya sa mace giwa ba ta yi haihuwa ba bayan kwanaki uku da wa'adin haihuwa ya cika.
Ma'aikata da yawa na gidan dabobi sun nuna damuwarsu kan giwar Man Ling wadda take da shekaru 21 da hahihuwa aka shigo da ita daga kasar Myanmar a shekara ta 1998.Darajar giwar nan ta kai kudin Sin RMB yuan fiye da miliyan daya.tsawnota ya kai mita 2.3,nauyinta ya kai TON.kwatankwacin tsawon rayuwar giwa ya kai shekaru saba'in.lokacin da jaririn ke zama a cikin giwa ya kai tsakanin watanni 20 da 22.
---Matan biyu sun yi fada a cikin bank.An tsare mata biyu sabo da suka yi fada a cikin banki domin amfani da injunan sarrafa alamun hada hadar kasuwannin kudade a Hongkong.
Wannan al'amari ya faru ne a ranar talata da ta shige a wurin Kwan Tong na yankin Hongkong.A cikin bankin nan da akwai injuna bakwai dake iya sarrafa alamun hada hadar kudaden kasuwanni da aka shirya domin mutane masu zuwa ba tare da biyan kudi ba.Mata biyu,daya sunanta Cheung mai shekaru 51 da haihuwa,dayan kuwa sunanta Mak,mai shekaru 58 da haihuwa,kowanensu na amfani da nata injin.Da matar Cheung ta gano injin Mak ya fi nata sauri,sai ta fara amfani da shi,Matar Mak ta yi fushi sai ta dagula shirye shiryen injin Cheung.Daga nan fada ya tashi tsakaninsu daya na jan gashi wata daban,wata kuwa ta ciji wata daban.
Duk da hak babu wanda daga cikin masu zuwan banki ya sassanta su,an ce matan biyu masu kudi ne suka zo bank ne da amfani da injuna yadda su ke ga dama ba tare da kula da saura ba.
Jama'a masu sauraro,kun dai saurari sabon shirin da muka kawo muku kan labaru masu ban sha'awa.Wannnan ya kawo karshen shirinmu na yau ku huta lafiya.(Ali)
|