Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-10 17:31:02    
An mayar da mutane a gaban kome a filin wasa na taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing

cri

A kwanan baya, an yi gasar wasannin kirket na makafi bisa gayyata a dakin wasa na Jami'ar fasaha da kere-kere ta Beijing, wadda ke daya daga cikin jerin gasar jarrabawa ta Goodluck Beijing, ita ce kuma gasa ta farko da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya shirya don jarraba ingancin filaye da dakunan wasa wajen shirya gasar wasannin Olympic na nakasassu. A cikin gasar da aka yi a wannan karo, a bayyane ne kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya nuna tunanin bai wa 'yan wasa da 'yan kallo nasakassu hidima daga dukkan fannoni.

Dakin wasa na Jami'ar fasaha da kere-kere ta Beijing zai shirya gasar wasan kwallon raga da wasannin kirket na makafi a shekara mai zuwa. Don shirya gasar jarrabawa yadda ya kamata, musamman ma bai wa 'yan wasa da 'yan kallo nakasassu kyakkyawar hidima, masu shirya gasar da kuma kungiyar tafiyar da harkokin dakin wasa na Jami'ar fasaha da kere-kere ta Beijing sun yi shiri na musamman.

A tashar bincike da ke kofar dakin wasa na wannan jami'a, domin an kera kekunan hannu da wasu nakasassu ke amfani da su da kuma gororinsu da sauran kayayyakin taimako da karfe, wadannan abubuwan karfe su kan kawo matsala ga ma'aikatan tsaro wajen yin bincike, shi ya sa masu shirya gasar suka zayyana hanyar musamman, inda ma'aikatan musamman suka yi bincike kan nakasassu tare da amfani da inji a hannunsu, a maimakon injin bincike.

A cikin wannan dakin wasa, an gyara dimbin matakalu zuwa gangara, haka kuma, ana iya ganin bayanan musamman na makafi a wurare da yawa. Darektan kungiyar tafiyar da harkokin dakin wasan nan malam Wang Changhe ya yi karin bayanin cewa,'Mun shimfida hanyoyin musamman na makafi a dukkan wuraren da 'yan wasa ke amfani da su. Ban da wannan kuma, baya ga bayanan Sinanci da Turanci, mun fito da bayanan musamman da aka yi wa makafi a Turance a wuraren da suka fi amfani da su.'

Ban da bayanan musamman na makafi, ma'aikatan dakin wasan sun manna 'yan guntuwar takarda a kan ko wace kwana a wannan dakin wasa, wadanda aka shafa abubuwan walkiya a kansu. Ta haka ana iya farga da makafin da ke iya ganin abubuwa kadan da su lura da kwana, kada su yi karo da bango. A sa'i daya kuma, ya zama wajibi dukkan masu aikin sa kai su sanya abun wuyan hannu da aka shafa abubuwan walkiya a kai, ta haka, wadanda ke iya ganin abubuwa kadan na iya ganin masu aikin sa kai cikin sauki, suna iya samun taimako daga wajensu.

Masu zayyana sun mayar da martabar mutane a gaban kome a fannin zayyana ban daki na jama'a na musamman a cikin dakin wasa na Jami'ar fasaha da kere-kere ta Beijing. Dukkan maza da mata na iya amfani da irin wannan ban daki na musamman tare, inda aka kafa shinge don hana ganin juna. Malam Wang ya yi bayani kan dalilin gina irin wannan ban daki na musamman, ya ce, 'Mutanen da suka nakasa a kafa ko a hannu, alal misali, masu shanyewar yawancin jiki ba za su iya kewaya da kansu ba, suna bukatar taimako daga wadanda ke rakiyarsu. Irin wannan ban daki na musamman na iya biyan bukatunsu, inda dukkan maza da mata da ke taimakawa masu shanyewar yawancin jiki na iya shiga a ciki.'

Baya ga na'urori masu inganci, fara'a da goyon baya da masu aikin sa kai ke nunawa na da muhimmanci sosai wajen shirya gasa yadda ya kamata. Nakasassu mutane ne da ke da bukatun musamman. Ba su kyakkyawar hidima ya bukaci masu aikin sa kai da su nuna fara'a da kuma taimakonsu bisa son rai, amma kada su sa hannu fiye da kima. Sa'an nan kuma, tilas ne su ba da hidima da idon basira. Malam Wang ya kawo mana wani misali, ya ce, 'Ga misali, in mai aikin sa kai ya ja gorar wani makaho zuwa kujera, saboda bai iya ganin kome ba, shi ya sa mai aikin sa kai na bukatar daddafa kujera tare da cewa, ita ce kujera, a maimakon cewar, ka zauna, ta haka wannan makaho zai gane.'

Ko da yake dakin wasa na Jami'ar fasaha da kere-kere ta Beijing ya sami babban yabo daga bangarori daban daban, amma game da abubuwan da ake bukatar a kyautata, malam Wang ya ce, 'Bayan da muka yi kimanta matsalolin dakin wasan, za mu kyautata abubuwan kasawa don raya dakin wasan zuwa matsayin da ya cancanta da kuma biyan bukatun taron wasannin Olympic na Beijing, musamman ma na nakasassu.'