Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-09 17:04:53    
Li Yuanchang wanda ke nuna kauna sosai ga ayyukan koyarwa na kauyukan kasar Sin

cri

A cikin dogon lokaci, makarantun kauyukan da ke yankuna marasa ci gaba na kasar Sin suna fuskantar matsaloli da yawa, kamar rashin kwararrun malamai wajen koyarwa da rashin kudin gudanar da harkokin makarantu da dai sauransu. Yaran da ke wadannan yankunan ba su iya samun nagartaccen ilmi kamar yadda takwarorinsu da ke biranen kasar Sin suke samu. Domin kyautata wannan halin da ake ciki, malamai da dimbin yawa suna bayar da gudummuwarsu wajen ayyukan koyarwa a kauyukan kasar Sin, Malam Li Yuanchang yana daya daga cikinsu. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani game da wannan mutum da kuma irin gudummuwar da ya bayar wajen yin gyare-gyare a harkar koyarwa a kauyuka.

Li Yaunchang dan shekaru 57 da haihuwa yana da zama a cikin wani kauye da ke jihar Jilin, ya gaya wa wakilinmu cewa, yana sha'awar karanta littattafai tun yarantakarsa, ko da yake zaman rayuwarsa ba shi da kyau sosai, amma bai yi watsi da ci gaba da karatu ba. Kuma bayan da ya gama karatunsa daga jami'a, ya kama harkar malanta ba tare da shakka ba. Haka kuma ya bayyana cewa, bisa matsayinsa na malami a kauye, abin da ya fi bakanta ransa shi ne wasu yara sun yin watsi da karatu sakamakon talauci. "dukkan 'yan makaranta da na koyar da su na dauke su tamkar yarana, sabo da haka nake tsayawa kan ra'ayin cewa, ya kamata a nuna kauna ga dalibai kamar yadda a kan yi ga 'ya'ya. Lokacin da na san Wani dalibina da ya yi watsi da karatu sakamakon talauci, na je gidansa har sau biyar ko shida don lallasar iyayensa da su sake mai da shi makaranta."

Li Yuanchang ya fara aikinsa na koyar da sinanci a wani makarantar sakandare ta yankin a shekara ta 1985. Kuma tun wancan lokaci. Ya fara neman yin gyare-gyare kan aikin koyar da sinanci da ya dace da halin da kauyuka ke ciki. Ya mayar da maka-makan kauyuka a matsayin babban ajin karatu, kuma ya karfafa gwiwar dalibansa wajen shiga harkokin aikatawa a fannin zaman al'umma. Malam Wang Wei wanda ke yin aiki tare da Li Yuanchang ya amince da wannan tunani sosai. "makasudin Malam Li kan ayyukan koyarwa shi ne horar da 'yan kwadago masu nagarta don amfanin garinsa. Sabo da haka kullum ya kan shigad da dalibansa a cikin zamantakewar al'umma domin su samu ilmi ta hanyar yin harkokin aikatawa."

Bisa labarin da muka samu, an ce, a cikin daliban da Li Yuanchang ya koyar a kauyuka, wasu dalibai sun shiga jami'o'i, wasu kuwa sun zama kwararru wajen fasahar shuke-shuke a wurin. Ban da wannan kuma an shigad da kasidar da dalibansa suka rubuta wadda ake kiranta "Furannin da ke kan maka-makan filayen gonaki" a cikin littafin koyar da sinanci na jihar Jilin. Yan Zhaodong, wani dalibin Malam Li ya gaya wa wakilinmu cewa, abin da ya samu daga Malam Li shi ne wata kwarewa da zai iya yin amfani da ita a duk rayuwarsa. "abin da Malam Li ya koyar mana ba ilmi kawai ba, har ma da wata dabara kan yadda za a samu ilmi. Wannan wata kwarewa ce da za a iya yin amfani da ita a duk rayuwarsa."

Amma abin bakin ciki shi ne, yau shekaru 6 da suka gabata, Li Yuanchang ya kamu da ciwo mai tsanani sosai, saboda haka tilas ya kaurace wa teburin lacca da dalibansa. Sakamakon la'akarin da aka yi kan lafiyarsa, shi ya sa hukumar kula da ilmi ta wurin ta tura shi zuwa kwalejin koyarwa na jihar Jilin wanda yanayinsa ya fi kyau domin yin aikin nazarin sinanci. Dalilin da ya sa aka yi haka shi ne Malam Li ba zai fuskanci aiki sosai ba, amma Li Yuanchang ya mai da wannan sabon aiki a matsayin wani sabon masomi na gudanar da ayyukan koyarwa na kauyuwa. "idan jikina ya samu sauki, to zan je kauyuka daban daban, sabo da aikina ya canja, yanzu ni wani manazarci ne na aikin koyarwa. A ganina, idan wani manazarcin aikin koyarwa ke son gudanar da aikinsa da kyau, to ya kamata ya fahimci halin ayyukan koyarwa da duk jihar ke ciki yanzu."

Sabo da haka, tun wancan lokaci, ya gudanar da aikinsa a cikin kauyuka kusan watanni hudu a ko wace shekara. Ya zuwa yanzu ya riga ya ziyarci makarantun sakandare da yawansu ya kai kashi 80 cikin dari da ke kauyuka da gudumoni na jihar. Ta yin nazari, Li Yuanchang ya gano cewa, rashin kwararrun makamai wajen koyarwa ya zama wani muhimmin abin da ya kawo cikas ga bunkasuwar sha'anin ilmi na kauyuka. Amma sabo da rashin kudi, ba a iya gudanar da ayyukan horar da malamai sosai ba. A wannan halin da ake ciki, Malam Li ya gabatar da wani tunaninsa wajen kafa sansanin kauyuka kan horar da malamai, ta yadda malamai na makarantu daban daban na kauyuka za su iya yin tattaunawa kan ayyukan koyarwa tare. A karkashin kokarinsa, an riga an kafa sananonin kauyuka guda 42 daya bayan daya a yankuna 9 na jihar, kuma matsayin malaman kauyuka da yawa ya inganta sosai sakamakon kwasa kwasai na horaswa da suka halarta.