Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-09 16:32:37    
Kasar Sin ta samu manyan nasarori a yunkurinta na tabbatar da zaman lafiya a duniya

cri

Masu sauraronmu assalamu alaikun, barkammu da wannan lokaci,sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirinmu na Mu leka a kasar Sin.A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayani kan nasarorin da kasar Sin ta samu wajen harkokin waje. A gabannin kiran babban taro a karo na 17 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin mai rike da mulkin kasar Sin, Waiwayen cigaban da aka samu a cikin shekaru biyar da suka gabata ya nuna samun nasarori a yunkurin tabbatar da zaman lafiya a duniya da Jam'iyyar kwamainis ta Sin ta gabatar ya zama wani jigon manufar harkokin waje ta kasar Sin. A cikin rahoton da aka gabatar a babban taron wakilan kasa a karo na 16 na JKS kafin shekaru biyar,an bayyana cewa "Muna so mu yi kokari tare da sauran kasashen duniya, mu nuna kwazo da himma wajen ganin duniya da ta sami rukunoni da kungiyoyi masu ra'ayi daban daban ke kasancewa tare cikin lumana. Kalmar "lumana " ko "sulhu" ta bullo a cikin manufar harkokin waje ta kasar Sin.A watan Satumba na shekara ta 2005,a gun taron koli na bukin cikon shekaru 60 da kafuwar Majalisar Dinkin Duniya,shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi jawabi mai muhimmanci wanda ke da lakabin kokarin shimfida wata duniya mai dauwamamen zaman lafiya cikin wadatuwa da jituwa tare.

Ya ce, " Ya kamata mu saka sabon ra'ayin tsaro wato na amincewa da moriyar juna da kuma taimakon juna tare da nuna daidaito, da amfani ga kowa da kowa. Ya kamata mu shimfida wani cikakken tsarin cinikayya na bude kofa da daidaito da rashin wariya tsakanin bangarori daban daban,

Kamata ya yi kasashe masu sukuni su dauki karin nauyi ga duniya wajen neman samun cigaba maidorewa, da ba da taimako ga kasashe matasa domin su gaggauta bunkasuwa ta yadda kowa da kowa zai iya ci moriyar cigaba a karni na 21.Ya kamata mu bi ka'idar daidaito da bude kofa, mu kiyaye banbancin dake akwai tsakanin al'adu,mu kara mu'amala da musanya ra'ayoyi tsakanin mu da kuma kokarin samar da wata duniya cikin sulhu da ta kunshi al'adu iri iri. Bisa tunanin nan, kasar Sin ta samu manyan nasarori a fannin harkokin waje.ta taka rawar a zo a gani wajen manyan batutuwa na duniya.

Kan batun makaman nukiliya na Korea ta arewa,kasar Sin ta kawo shawarar tattaunawa tsakanin bangarori shida,ta mayar da batun nan kan hanyar ci gaba yadda ya kamata,har ma ya samu babban cigaba.Kan batun yankin Darfur na kasar Sudan,kasar Sin ta taka rawa mai amfani,ta gaggauta neman gwamnatin Sudan da ta hada kanta da MDD da Tarayyar hadin kan Afrika wajen yin shawarwarin zaman lafiya, Kasar Sin ta ba da taimakon jin kai sau da dama ga yankin Darfur da tura dakarunta wajen kiyaye zaman lafiya a wannan yanki.Ban da wannan kuma kasar Sin ta tura dakarun kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Liberia da Lebanon da sauran kasashe takwas,kasar Sin ta shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD ta shirya a wadannan wurare. Kan batun nukiliya na kasar Iran,kasar Sin ta yi ayyuka da dama na yin lallashi da gaggauta yin shawarwari. Ana iya jin duriyar kasar Sin a babban taron MDD da kungiyar APEC da tattaunawa da kungiyar group 8 da taron koli na Asiya da Turai da kuma kungiyar hadin kai ta Shanghai da taron koli na Beijing kan tattaunawa tsakanin Sin da Afrika da batutuwan da suka shafi yaki da 'yan ta'adda da sauyin yanayi da makamashi. A ganin profesa Mr Zhu Feng na jami'ar Peking,kasar Sin ta bayar da muhimmin taimako ga zaman lafiya a duniya.Ya ce"Kasancewar duniya cikin sulhu wani jigo ne na manufar harkokin waje ta kasar Sin.Alkibla ce da kasar Sin take bi wajen tafiyar da harkokin waje cikin halin duniya da muke ciki.A kan matsayin babbar kasa mai dauke da alhakin dake bisa wuyanta,kasar Sin ta yi niyya da imani wajen ciyar da duniya gaba wajen samun zaman lafiya da hadin kai.

ProfesaGupta na jami'ar Maryland ta Amurka ya ce  "A ganina,ra'ayin samun duniya cikin sulhu ya dace da ra'ayin samun ci gaba cikin lumana.Samun cigaba cikin lumana yana nufin a shimfida kyakywar dangantaka tsakanin Sin da sauran kasashen duniya.Ra'ayin samun ci gaba cikin lumana yana nufin cewa bangarori biyu suna samun ci gaba,.Ci gaban kasar Sin ba ya nufin cewa sauran kasashen duniya sun yi hasara." Jakadan kasar Syria a kasar Sin Mr Kheir Al-wadi ya ce "ra'ayin kasar Sin na samu duniya cikin sulhu yana taimakawa wajen shimfida zaman lafiya a duniya.Ya ce shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kawo ra'ayin samun duniya cikin sulhu ne tare da zummar kare zaman lafiya da kasancewar al'adu iri iri cikin lumana a duniya.Wannan ra'ayin yana amfanawa dukkan kasashen duniya da ci gaban zaman Bil Adam. Jama'a masu sauraro,kun dai saurari bayani kan ra'yin samun duniya mai sulhu da kasar Sin take rike da shi kan halin da muke ciki a duniyar yau. Mun gode muku sabo da kuka saurarenmu.(Ali)