Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-08 18:33:05    
Yanzu kuma za mu karanta muku wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin.

cri

---- An samu labari a ran 10 ga watan Satumba cewa, hukumar shiyyar Naqu da ke jihar Tibet ta yi shirin ware kudin kasar Sin wato Yuan miliyan 590 don mai da makiyayan da yawansu ya kai kashi 80 bisa 100 da su daina yawo da dabbobi bayan shekaru 3 masu zuwa, kuma su zauna cikin sabbin dakuna masu tsimi da zaman lafiya kuma masu amfani.

Mr. Duotuo, gwamnan hukuwar shiyyar Naqu ya bayyana cewa, a lokacin shiri na 11 na shekaru 5 na raya kasa, shiyyar ta yi shirin ware kudin kasar Sin wato Yuan miliyan 590 da za a samu daga jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta da shiyyoyi daban-daban da ke karkashin shugabancinta, kuma daga kudaden da aka samar don ba da taimako ga jihar Tibet, ta yadda zuwa karshen lokacin shiri na 11 na shekaru 5 na raya kasar, za a yi kokarin tabbatar da makiyayan da yawansu ya kai kashi 80 bisa 100 ko fiye na duk jihar, wato yawan iyalan makiyaya ya wuce 50,000 za su daina yawo da dabbobi, su zauna a wuri guda.

---- An samu labari a ran 9 ga watan Satumba daga birnin Tananarive, babban birnin kasar Madagascar cewa, a wannan rana da yamma, kungiyar 'yan fasaha na kabilun kasar Sin ta nuna wasanni masu sha'awa irin na kabilun kasar Sin, daga nan ne aka bude wasannin da kungiyar 'yan fasaha na kabilun kasar Sin ta nuna a kasashe 4 na Afirka wadanda ofishin kula da harkokin Sinawa mazauna kasashen waje na majalisar gudanarwa ta kasar Sin da hadaddiyar kungiyar kasar Sin ta yin mu'amala tare da kasashen ketare suka shirya tare.

Kungiyar 'yan fasaha ta kabilun kasar Sin tana kunshe da 'yan fasaha mafiya kwarewa na kasar Sin, ciki har da Yang Jiqiang, mai gurza kukuma iri ta kasar Sin da shahararren mawaki Cheng Zhi da zabiya Dong Wenhua wadanda suka nuna wasanni masu ban sha'awa domin 'yan kallo, wakoki masu dadi da suka rera, da kide-kide masu ban sha'awa da suka yi, da wasan dabo mai ban mamaki sosai da suka nuna sun samu kyayyawar maraba daga wajen Sinawa mazauna kasar Madagascar da mutanen Madagascar 'yan asalin kasar Sin da 'yan kallo na wurin.

---- Kwanan baya a gundumar Alashan ta dama ta jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta, an fara gina wani babban dakin adana zane-zanen duwatsu wanda fadinsa ya kai murabba'in mita 2000 domin ba da kariya ga zane-zanen da aka yi kan tsaunin Mandela wanda ya shahara a duniya.

Bisa kididdigar da aka yi an ce, yawan zane-zanen duwatsun da ke kasancewa yanzu a tsaunin Mandela ya kai 4234, wadanda suka siffanta yadda makiyaya suke yin farauta da kiwon dabbobi.

Jama'a masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirin "Kananan kabilun kasar Sin." daga nan Sashen Hausa na Rediyon kasar Sin. Umaru ne ke cewa assalamu alaikum. (Umaru)