
An kaddamar da cibiyar watsa labaru ta babban taro na 17 na wakilan kasa na JKS a ran 8 ga wata da safe a hukumance. A halin yanzu dai 'yan jarida na kasashe da yankuna 42 da yawansu ya kai 1033 sun yi rajistar sunayensu don neman labaru kan babban taron, wadanda suka shafi kafofin watsa labaru 258 a ciki har da 'yan jarida 342 da suka zo daga Hongkong da Makau da Taiwan.

An kafa cibiyar watsa labaru ta babban taron a Media Centre a Beijing. Cibiyar watsa labarun za ta yi ayyukan baiwa 'yan jarida na kasashen waje takardun shaida da karbar tambayoyin da kafofin watsa labaru na kasashen waje suka yi da bayar da sanarwa da shirya taron manema labaru da dai sauransu.
Zhai Huisheng, shugaban cibiyar watsa labaru ta babban taron ya nuna cewa, cibiyar za ta yi kokari don bayar da hidimar mutunci ga 'yan jarida a fannonin neman labaru da bayar da labaru da dai sauransu.(Zainab)
|